Gwamnatin haramtacciyara kasar isra’ila ta haramtawa iyalan wadanda take tsare dasu a gidaje fursunan ta ziyatara ‘yan uwan su bayan da aka samu uku daga cikin wadanda ke tsare a gidan fursuna mai cikakken suka tsere kuma jami’an tsaron haramtacciyar kasar isra’ilan suka kasa kamo.
Hukamar gidan yarin na haramtacciyar kasar isra’ila sun bayyana haramtawa iyalan wadanda ke tsare a fursin din ziyartar su hara zuwa karshen wannan watan amma sai dai kungiyar masu rajinkare hakkin fursunonin falasdinu sun koka dangare da lamarin inda suka bukaci hukumomi da duniya su sanya baki cikin lamarin domin\ karshen tauye hakkin da isra’ilan takewa fursunonin da ta kama kuma take tsare dasu.
Isra’ila ta bayyana daukan wannan mataki ne bayan hatsaniya data auku sakamakon kubutar fursunonin guda uku wanda dan tsatsaturan ra’ayin firayi ministan kasar Naftali Bennett ya bayyanara a matsayin babbar matsala.
Wannan dai shine daya daga cikin manya manayan nasarorin da falasadinawa suka taba samu na kubuta daga gidajen yarin haramtacciyar kasar isra’ilan tin bayan kubutar da falasdinawan suka taba yi daga gidan yarin isra’ila a shekarar 1987.
Rahotanni dai sun tabbatar da cewa tun bayan kubutar fursinonin jami’an tsaron haramtacciyar kasar isra’ila sun tsaurara takurawar su ga fursunonin dake gidajen yarin su musamman wadanda ke gidajen yarin Negev, Ofer, Gilboa, da kuma Ramon.
Daga cikin matakan rashin imanin da israilan ta dauka a kan dubunnan fursinoni falasdinawa har da kokarin rarraba fursinoni 400 wadanda suke da alaka da kungiyar jihadul isalam zuwa gidajen fursuna mabambanta.
Watan mataki mai ike da zalunci ya harzuka fursunonin musamman a gidajen fursin din Negev na Ramon inda ta kai wasu daga cikin fursunonin sun fusata sun fara cinna wuta a wasu bangarori na gidan fursun din.
Yanzu dai kungiyar fursunoni da kuma tsaffin fursunoni ta falasdinu ta ja kunnen isra’ila kan sake dagula al’amura bayan yanayin da ake ciki a yanzu.