Wannan shine karo na biyar da kasar isra’ila ke shirin shiga kakar zabe a kasa da shekara hudu da suka gabata, a inda yahudawan sahayoniya zasu kara kada kuri’un zaben majalisar kasar a karo na biyar a kasa da shekaru hudu, wannan yanayi na rashin tsari a lamurran zaben kasar ta yahudawan sahayoniya na iya sanya shakku gami da tambayoyi a zukatan mutane dangane da tsarin siyasa a kasar.
Kasar Isra’ila na bin tsarin mulkin da ake ma laqabi da ”Paliamentary System” ma’ana tsarin majalisa kuma kasar tana da jam’iyyun siyasa mabambanta amma a duk zabubbukan da ake gudanarwa babu ja’iyyar da ta taba iya samun kuri’u masu yawan da zasu bata damar samun rinjayen da zata iya karbe jagorancin kasar mai cike da yahudawa.
Wannan ya tilastawa jam’iyyu su hade waje daya domin samun karfin da zasu iya samar da kujeru 61 a majalisar kasar wanda zai basu damar kafa gwamnati.
Wannan hadakar kuma tana iya samun matsala wanda zai kai ga rasa goyon bayan wata jam’iyyar hakan kuma zai sabbaba rashin samun nasarar samun kujerun da zasu sabbaba kafa gwamnati ga jam’iyya.
Babbar fuska a kasar wanda ya shafe lokaci mafi tsawo yana firayi minista a ‘yan shekarun daya shafe yana shugabancin kasar, ya lalata tsarin sakamakon shahara da yayi da rashin gaskiya gami da cin hanci da rashawa.
A gefe guda kuma mazauna Isra’ila na fuskantar matsalar bakunta a sansanin da suka kwace daga hannun raunana falasdinawa kuma suka sanyawa wajen suna Isra’ila suke rayuwa a wajen alhali ‘yan asalin halaliyar wajen suna gefe suna kallon su.
Ko a ranar litinin 30/10/2022 ma sai da raunanan falasdinawa suka gudanar da gangami a ”west bank” da kuma Alquds domin nuna kin jinin zaluncin da shugabannin sansanin kasar Isra’ila ke musu gami da nuna goyon bayan su ga mutanen Alquds wadanda Isra’ilan ke zalunta.