Tun a safiyar ranar juma’a aka shaidi gangankon iraniyawa a cibiyoyin kada kuri’a domin zabar sabon shugaban kasa, bincike ya tabbatar da cewa duk da an tsara za’a fara gudanar da zaben ne da karfe bakwai na ranar juma’a wanda yayi dai dai da 18 ga watan june 2021 amma tun cikin dare iraniyawan suka fara tururuwa zuwa cibiyoyin kada kuri’u a garuruwan su domin kama layi.
Safiyar juma’a 27 ga khordad a lissafin shekarar iraniyawa tazo da babban tarihi inda a kalla ‘yan jarida dari biyar daga kasashe fiye da dari biyu suka bakunci kasar domin shaida wannan zabe mai matukar muhimmanci ga al’ummar Iran dama duniya baki daya.
Jagoran juyin juya halin musulunci na jamhuriyar musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamne’e shine ya fara kada kuri’ar sa dai dai karfe bakwai na safe wanda aka haska kai tsaye a kafafen sadarwa na cikin gida Iran dama sauran duniya, hakan kuma shine ya tabbatar da fara kada kuri’u a aikace a fadin kasar ta jamhuriyar musulunci ta Iran.
Duniya Ta Shaidi Zaben Da B’a Taba Irin Sa Ba A Tarihi.
Al’ummar duniya musamman masu bibiyar al’amuran siyasar duniya sunyi mamakin yadda iraniyawa sukayi fitar farin dango zuwa ga kada kuri’un su, wanda hakan ya sanya dole hukumar zaben kasar ta Iran ta kara lokacin kada kuri’un daga karfe goma zuwa sha daya na dare, bayan na ta kuma karawa zuwa sha biyu na dare amma duk da haka Iraniyawa da yawa dai suna kan sahun kada kuri’a wanda hakan ya tilasta wa hukumar zaben ta sanar da cewa ta bada damar da Iraniyawan su cigaba da kada kuri’u har lokacin da kowa zai kada kuri’ar sa koda kuma za’a kwana a wuni ne, al’amarin da yasa akayi zaben da ba’a taba irin sa ba a tarihin duniya inda aka wuni aka kwamna ana kada kuri’a.