Juma’a 4 ga Octoba na shekarar 2022 itace tayi dai dai da 13 ga watan Aban a shekarar shamsiyya kuma wannan rana itace ke zaman ranar yara ‘yan makaranta a wajen Iraniyawa kuma a ranar ne Iraniyawan musamman yara ‘yan makaranta ke fitowa domin jaddada goyon bayan su ga nizamin musulunci gami da nuna kin jinin su ga Amurka da kawayen ta.
A wannan shekarar ma Iraniyawan basuyi kasa a gwuiwa ba sun fito a miliyoyin su a garuruwa fiye da dari biyu na kasar musamman babban birnin Tehran domin nunawa duniya cewa suna tare da nizamin musulunci na Jamhuriyar Musulunci ta Iran din.
Rahotanni sun tabbatar da cewa duk da matsin tattalin arziki da Iran din ke fama dashi wanda sakamakon takunkuman tattalin arziki da Amurka da kawayen ta suka kakaba ne, gami da kokarin gurbata tunanin Iraniyawan da kafafen yada labaran kasashen yammacin turai sukeyi amma hakan bai hana Iraniyawa fitowa domin goyon bayan nizamin sun na Islama ba.
A yau juma’a an gano shugaban kasar Iran Dakta Ibrahim Ra’isi a cikin miliyoyin Iraniyawa a daya daga cikin manyan titunan Iran yana mai cewa ”Iran ta jima da samun ‘yanci daga hannun bakin zaluncin Amurka kuma Iraniyawa basu shirya sake zama saniyar tatsar Amurkan ba”.
Ra’aisi yana mai bada amsa ne ga wani jawabi da shugaban amurka joe biden yayi wanda yake nuna suna son ‘yanto Iran din.
A bayanin sa Ra’isi ya bayyana biden yayi wannan jawabi ne a cikin rikicewa kamar yadda ya saba domin Iraniyawa sun jima da samun ‘yanci fiye da shekara arba’in da suka wuce tun zamanin gwagwarmayar Imam Khumaini (Q.s).
Iraniyawa dai na amfani da ranar 13 ga Aban domin tabbatarwa da duniya cewa bafa sa tare da Amurka kuma ba sa maraba da duk wani salon zalunci da zai fito daga amurkan.
Miliyoyin Iraniyawan dai sun dingi nuna bacin ransu dangane da takunkuman zalunci da amurka ke kakabawa kasar ta su.