Iran ta bayyana kokarin da amurkan keyi na tabbatar da cewa hare haren da ta kai kan ‘yan kasa a iyakar siriya da iraqi yana kan ka’ida.
Iran ta bayyana kokarin da amurkan keyi na tabbatar da hare haren a matsayin suna bisa kan ka’ida a matsayin marassa tushe balle makama.
Hare haren wanda yayi sanadiyar rasa rayuka kusan biyar ciki har da jariri ya janyo hankalin kafafen watsa labaran duniya inda masu sharhi kan lamuran siyasar duniya suka fara nuna damuwar su dangane da yadda amurkan ke gudanar da hare hare a kasashen yankin gabas ta tsakiya ba tare da kura da kiyaye dokokin kasa da kasa kamar yadda majalisar dinkin duniya ta tabbatar ba.
Ita dai amurka tayi ikirarin cewa wannan harin na ramuwa ne inda tayi zargin cewa wadanda ta kaiwa harin suna goyon bayan Iran, duk da ta tabbatar da cewa ‘yan asalin kasashen siriya da iraqi ne amma a cewar amurkan kungiyyin suna goyon bayan jamhuriyar musulunci ta Iran wanda hakan a ganin amurkan babbar barazana ce a kasancewar ta a yankin na gabas ta tsakiya mai yawan arzikin man fetur.
Tuni dai kasashen duniya ciki har da rasha, china da Iran sukayi Allah wadarai da hare haren rashin imani da amurkan ta kai kan ‘yan kasa a iyakar siriya da irakin.
Gwamnatin shugaba joe biden dai an sa ran zata rage takalar Iran din fada sakamakon yadda tsohon shugaba Trump ya lalata alakokin amurkan da kasashen duniya amma sai dai ga dukkan alamu itama gwamnatin shugaba joe biden kamar ci gaba ne daga inda tsohon shugab trump ya tsaya domin kusan duk kuasa kuran da shugaba trump ya aikata a tsahon shekara hudiu na mulkin sa shi sabuwar gwamnatin shugaba joe biden take maimaitawa.
Mutanen iraqi da siriya dai sun jima da kokawa dangane abinda suke kira zalunci da amurkan ta aiwatar a kansu kuma basu ji ba basu gani ba,