Jamahuriyar musulunci ta Iran ta tura da kayayyakin bukata dana magunguna zuwa makociyar ta Afganistan sakamakon wata gagarumar girgizar kasa da aka wayi gari da ita wacce ta hallaka fiye da mutane dubu a afganistan din.
Ofishin diflomaisyyar Iran dake kabul babban birnin Afganistan din ne ya sanar da hakan, inda ya tabbatar da cewa jirage biyu cike da kayayyakin taimako wadanda suka hada da magunguna sun isa Afganistan din.
Sa’annan Iran din ta bayyana jimami gami da jajantawa ga mutanen Afganistan din.
Akalla dai mutane 1000 sun rasa rayukan su yayin da fiye da 1500 suka samu raunuka sakamakon yanayin girgizar kasa mai karfin 5.9 ya faru a gabashin afganistan din.
Adadin wadanda suke mutuwa sakamakon girgizar kasar yana cigaba da karuwa ayau laraba amma jami’an bada agajin gaggawa sun bayyana tsaunukan dake kewayen da lamarin ya faru domin ceto wadanda ke da sauran lumfashi.
Shugaban taliban ya nemi kasashen duniya su taimakawa afganistan din domin rage radadin wannan masifa da ta fadawa al’ummar ta Afganistan.
Hukumomi sun tabbatar da cewa daruruwan gidaje ne suka rushe sakamakon girgizar kasar.
Afganistan dai na cikin kasashen da ke fama da tashe tashen hankula gami da rashin tabbas tun bayan shigar sojojin amurka kasar a shekarar 2001.
Fatattakar amurka daga kasar da akayi a shekarar da ta gabata bai sanya an samu cikakken kwanciyar hankali ba amma an samu sassaucin barazanar rayuwar al’umma amma sai dai amurkan ta rike miliyoyin daloli mallakin afganistan din inda hakan ya jawo cece kuce yayin da al’ummar ta afganistan ke kallon hakan a matsayin tsantsan zalunci kuma sukayi kira ga amurkan da ta saki wadannan makudan kudade domin amfabar da al’ummar afganistan din ko a samu sassaucin tsananin da ake ciki a kasar.
Amma sai dai ga dukka alamu amurkan bata da shirin sakin wadancan makudan daloli duk da matsanancin halin da afganistawan ke ciki.