Ministan makamashi na kasar rasha Nikola Shulgrov ya tabbatarwa da manema labarai cewa kasar sa da kuma kasar Iran suna da babbar dama ta yaki ta takunkuman zalunci da kasashen yamma suka kakaba musu idan sukayi aiki kafada da kafada a fannonin makamashi da mai.
A wani zaman tattaunawa da jakadan irana moskow babbar bisrnin rasha, kazem jalali a ranar juma’a, misnistan makamashin na kasar rasha ya yabawa kasar jamhuriyyar musulunci ta Iran kan yadda take samun cigaba cikin gaggawa a bangarori da dama kuma ya bayyana hakan a matsayin lamari mai matukar muhimmanci domin tabbatar da cewa takunkuman zalunci da kasashen yamma suke sanyawa kan kasar basuyi wani tasiri ba.
Ministan ya bukaci gwamnatin Iran da rasha su kara karfafa alakar da suek da ita ta tattalin arziki domin fada da matsalolin da kasashen yamma ke kokarin haifarwa ta hanyar kakaba takunkuman tattalin arziki a kan al’ummomin kasashen biyu.
Ministan ya cigaba da cewa kasashen suna iya bunkasa tattalin arzikin su ba tare da dogara da kasashen yamma ba, inda ya bayyana gaskiya ma dai kasashen yammaci ne ke bukatar kasashen asiya maimakon kasshen aiya su bukaci kasashen yammaci wanda hakan gwamnatoci da dama a yankin ai=siya suka kasa fuskanta,.
Y bayyana cewa rasha a shirye take ta bada hadin kai domin karfafa kyakykyawar alakar tattalin arziki da sauran bangarori dake tsakanin kasashen biyu.
Ministan ya bayyana cewa a halin yanzu a kwai hadin gwuiwa tsakanin kasashen biyu a bangaren, makamashi,mai,da kuma titin layin dogo.
A nasa bangaren ambasadan Iran a rasha, Jalili ya bayyana cewa Iran da rasha sun jima da alaka mai kyau a bangarori da dama kuma ya tabbatar da cewa sabuwar gwamnatin Iran wacce zata fara aiki nan da ‘yan kwanaki zata dora daga inda tsohuwar gwamnatin da tsaya domin tababbatar da bunkasar alakoki tsakanin kasar sa da kuma rasha .