Mnistocin harkokin kasashen waje na kasar jamhuriyar musulunci ta Iran takwaran sa da rasha sun bukaci a kafa nagartacciyar gwamnati wacce zata hada dukkkan banagarorin al’ummu na kasar afghanistan wacce yaki ya jima da jikkata kasar amma kuma yanzu kungiyar taliban ta karbe iko a kasar.
Hossein Amir-Abdollahian da takwaran sa Sergei Lavrov na rasha sun bayyana hakan ne a wata fira da sukayi ta wayar tarho inda suka tattauna sabbin lamurran da suke faruwa a yankin asiya dama afghanistan din.
Hosssain Abdullaahian da Sergei Lavrov sun bukaci a kafa hadaddiyar gwamanti wacce zata hada kowanne bangaren siyasa, kabilu da kuma al’umma.
Yanzu hakan dai afghanistan na karkashin ikon kungiyar taliban wacce ta taba rike ikon kasar shekaru sama da ashirin da suka wuce, kafin sojojin amurka su fatattake su bayan harin 11 ga satumbar 2001 sakamakon kutse da sojojin amurkan sukayi a kasar ta afghanisatn.
Matsayar Iran dai danagane da kwace ikon da kungiyar taliban da kuma yi a afghanistan bai wuce kira da a kafa hadaddiyar gwamanati wacce bata wariya tsakanin afghanistan, inda kuma Iran din ta bayyanar kayen da amurka ta sha a afghanistan din a matsayin wata ‘yan manuniya da take nuna cewa al’ummar afghanistan suna da karfin zuciya da turjewa duk wani salon da bakin haure ‘yan mamaya.
Iran ta bukaci a tattabar da an kafa gwamanati wacce ba zata bama kasashen ketare damar shiga kasar afghanistan su maimaita abinda amurka tayi na tsawon shekara ashirin ba.
Tuni dai kungiyar taliban ta sanar da kafa sabuwar gwamnati inda ta bayyana nadin sabbin mukaman gwamnati kuma da tabbatar da fara aikin wadannnan mukamai ba tare da bata lokaci ba.
Sai dai gwamantin amurka karkashin jagorancin joe biden ta nuna rashin gamsuwar ta da sabuwar gwamnatin ta afghanistan wanda ake ganin sakamakon radadin shan kaye ne da amurkan tasha a kasar ta afghanistan bayan shafe shekaru ashirin tana mamayar kasar amma ta fice ba tare da cimma muradan ta ba.