Kungiyar masu fafutukar kafa ƙasar Biafra (IPOB) ta buƙaci shugaba Mohammadu Buhari da ya sake duba matsayarsa ta baya-bayan nan game da sakin shugabanta da ke tsare, Nnamdi Kanu.
Sai dai a wata hira da gidan Talabijin na Channels, shugaban ya sauya matsaya, yana mai cewa ya kamata shari’ar cin amanar ƙasa da ake yi wa Kanu ta ci gaba da gudana.
Sai dai a wata sanarwa da ta fito daga sakataren yaɗa labaran IPOB Emma Powerful, ƙungiyar ta zargi wadanda ta kira wasu mayaudara a kasashen waje da makiyan gwagwarmayar da take yi da alhakin sauya matsayar da Buhari ya yi.
Ta roki shugaban da kada ya saurari irin waɗannan mutane ya yi abun da ya dace.