Sarkin Ife, Adeyeye Enitan Ogunwusi ya na cikin wadanda suka fito a wasan fim na ‘Take me home’.
Mai martaba ya nuna al’ada da sarautar kasar Yarbawa a wannan wasa da aka shirya a Hollywood.
Wannan ne karon farko da babban Basaraken mai shekaru kusan 50 zai bayyana a wasan kwaikwayo.
Mai martaba Adeyeye Enitan Ogunwusi ya fito a wani shirin wasan kwaikwayo, wanda shi ne karon farko da Sarkin Ife ya shiga fim.
Jaridar Aminiya ta kawo rahoto a karshen makon nan cewa Sarkin Ife yana cikin taurarin fim dinnan na ‘Take Me Home’ da aka shirya a Hollywood.
A wannan fim da aka yi a kasar Amurka, Sarkin Ife,Adeyeye Enitan Ogunwusi ya fito a matsayin da ya dace da shi na babban Basaraken kasar Yarbawa.
An shirya wannan fim ne a birnin Kalifoniya a kasar Amurka a karkashin masana’antar Hollywood da aka kafa shekaru fiye da 110 da suka wuce.
Kamar yadda rahoton ya bayyana, fitowar mai martaba a wannan fim zai karawa masana’antar Amurkan kima, daraja da martaba a idon Duniya.
Wasan ‘Take me Home’ Jaridar nan ta Premium Times ta ce wannan wasan kwaikwayo na ‘Take me Home’, ya nuna irin tasirin al’adar Yarbawa a kasashen yammacin Duniya.
A shirin, an yi yunkurin nuna al’adar mutanen Afrika da irin jajircewa da yarda da kansu.
Abin da ya faru a fim din shi ne wasu mutanen kasar Amurka sun samu kan su a wani irin hali bayan diyarsu ta sanya rigar mutanen Ile-Ife da aka sato.
Wannan lamari ya jefa iyayenta da daukacin dangin Amurkawa a cikin matsala musamman bayan alkawarin da wasu mutanen Afrika suka yi masu.
Dotun Taylor wanda masanin tarihi da al’adu ne ya shirya wannan fim mai dauke da ban dariya da abin tsoro wanda zai kayatar da farare da bakaken fata.
A fim din akwai taurari irinsu, Dave Sheridan, Amber Rivette, Felissa Rose, da Meji Black.
Akwai su Abdullateef Adedimeji da Bayo Bankole (Boy Alinco).
Source:LegitHausa