A kwanakin baya ne minmistan harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran, Amir Abdullahiyan ya kai ziyarar aikin nahiyar Afirka inda ya zagaya kasashe mabambanta domin jaddada hulda tsakanin jamhuriyar musulunci ta Iran da kasashen na Afirka.
Ministan harkokin wajen Iran Amir Abdullahiyan ya ziyarci kasashen Mali, Tanzania da kuma Zanzibar a wannan rangadi wanda yayi a nahiyar ta Afirka.
Bisa wannan kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran a wata fira da manema labarai ya bayyana makasudi gami da hadafin wannan tafiya da Abdullahiyan.
A firar jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci Ta Iran mista Kanaani ya bayyana muhimman batutuwa dangane da tafiyar.
Kakakin ya bayyana nahiyar Afirka a matsayin nahiya mai matukar muhummanci gami da tasiri kuma ta tattara manyan mutane masu kokarin gwagwarmaya gami da ana zaluncin azzaluman gwamnatoci a duniya.
A ranar asabar din data gabata kanaani ya shelanta cewa zasu mayar da hankali kan alaka da nahiyar ta Afirka, inda kum aya bayyana hakan a matsayin muhimmin aikin da ma’aikatar hanrkokin wajen Iran din ta sanya gaba.
Jamhuriyar Musulunci Ta Iran dai na zaman kasa mafi karfin fada aji a nahiyar Asiya, tattare da barazanar kasashen yammacin turai amma hakan bai hana Iran din shimfida karfin fada aji dinta a yankin Asiya ba.
Idan Iran ta samu kwatankwacin tasirin data a samu a Asiya, a nahiyar Afirka hakan zai zama babbar barazana ga kasashen yammacin turai wadanda suke tatsar adadi mafi tsoka da arziki daga nahiyar Afirka mai yawan ma’aidanai da arzikin karkashin kasa.
Nahiyar Afirka wacce ke karkashin babakern turawa tun zamanin mulkin mallaka har zuwa yau.
Iran ta shahara da kalubalantar kasashen yamma bisa rashin kyautawar su a kasashen duniya wanda ake kallon hakan zaiyi tasiri ga afirkawa sosai musamman a matsayin su na wadanda suke kallon kansu matsayin wadanda turawan yamma sukafi zalunta fiye da kowa.