Kungiyar neman ‘yanci ta, hamas falasdinu tayi Allah wadarai da sabbin hare haren ta’addancin sojojin haramtacciyar kasar isra’ila a kan falasdinawa.
Kungiyar ta hamas a ta baki mai magana da yawun ta Hazem Kasem ta tabbatar da cewa tsanantar hare hare sojojin haramtacciyar kasar ta isra’ila bazai hana falasdinawa kokarin su na tabbatar da ‘yancin kasar falasdinu ba.
A asabar din data gabata ne dai sojojin haramtaccciyar kasar isra’ila ta kai wasu hare haren ba sani ba sabo yankin zirin gaza wanda yayi sanadin raunatar da dama kuma ya sabbaba asarar rayuka da dama.
”utanen mu zasu cigaba da kokarin ayyukan neman ‘yanci bisa doka kuma yadda ya kamata domin tabbatar da cewa sun ‘yanto kasar su daga hannun yahudawan sahayoniya” kasar yadda wani babban jami’in kungiyar ta hamas ya tabbatarwa da manema labarai a safiyar yau lahadi.
Ita dai isra’ila tayi ikirarin cewa hare haren nata ta kaisu ne a wasu bangarori mallakar kungiyar hamas wanda hakan ta tabbata kuskure ne domin mafi yawancin wadanda hare haren suka shafa fararen hula ne kuma raunana falasdinawa.
Wannan harin dai ya saba da alkawarin tsagaita wuta da aka cimma tsakanin gwamnatin haramtacciyar kasar isra’ila da kungiyar neman ‘yanci ta hamas a watan mayu da ya gabata bayan shafe tsawon kwanaki sha biyu ana gwabza yaki tsakanin bangarorin biyu.
Yakin dai wanda aka shafe tsawon kwana goma sha biyu ana yi ya tabbatar da gazawar sojojin isra’ila kuma ya nunawa duniya cewa kungiyar neman ‘yanto falasdinu ta hamas zata iya tarar duk wani kalubale daga haramtacciyar ta isra’il inda a karshe isra’ilan ta karbi tayin tsagaita wuta da kasar misra tayi mata ba tare da kowanne irin sharadi ba.
Masani masu sanya idanu a kan lamurran siyasar duniya sun tabbatar da cewa haramtacciyar kasar isra’ilan ta kwashi kashin ta a hannu a wannan yakin inda a karshe ta nemu sulhu ba tare da ta cimma hadafin ba.