Rahotannin dake shigo mana shine gwamnatin tarayyar najeriya tana cikin babbar matsala sakamakon awa arba’in da hudu da gamayyar lauyoyin ingila suka bata ta saki shugaban kungiyar ‘yan biyafara din idan kuma ba haka ba zasu dauki matakin daya dace a kan gwamnatin ta shugaba muhammadu buhari.
Kasar ingila dai tana da babban tasiri a lamuran gudanarwar najeriya domin itace tayi ma najeriyar mulkin mallaka saboda ana ganin wannan barazana daga gamayyar lauyoyin kasar ingilar a matrsayin wata gagarumar matsala wacce gwamnatin ta najeriya karkashin jagorancin shugaba muhammadu buhari ka iya fuskanta.
Tun da farko sabon firaministan haramtacciyar kasar isra’ila ya koka dangane da kama namdi kanu din inda ya bayyana kamun a matsayin baya bisa ka’ida kuma ya bayyana kanu din a matsayin babban gwarzo, sa’annan firaministan haramtacciyar kasar isra’ilan ya bayyana cewa gwamnatin sa zatayi duk mai yiwuwa domin kwato namdi kanu daga hannun gwamnatin tarayya.
Tashar yada labarai mallakin magoya bayan namdi kanu ta linda T.v news ta wallafa wannan labari wanda ya dauki hankalin mutane mutane inda ta bayyana cewa lauyoyin na kasar ingila sun bawa gwamnatin najeriya awa ashirin da hudu ta saki shugaban na masu rajin kafa kasar biyafara ko kuma su dauki mataki a kan lamarin.
Tuni dai ta bayyana cewa namdi kanu wanda aka kamo bayan ya arce daga najeriya lokacin da aka bada belin yana da goyon bayan wasu daga cikin kasashen ketare wanda hakan ke nuna da yiwuwar suyi uwa suyi makarbiya domin fitar dashi daga hannun hukumomin najeriya.
Lauyan kanu dai ya tabbatar da cewa zuwa yanzu ba’a barsu sun gana da wanda suke wakilta ba amma suna bin duk hanyoyin da suka dace domin tabbatar da halin da kanu din yake ciki.
A gefe guda kuma yau ne aka gudanar da shari’ar shugaban darikar shi’a na najeiya malam ibrahim zakzaky wanda ake tsare dashi ba bisa ka’ida ba kuma ba tare da ya aikata laifin komi ba.