Gomomin dubunnan al’ummar kasar Yemen ne suka shiga gangamin nuna bacin rai dangane da kone Al’qurani da wasu sukayi a birnin Stockholm na kasar Sweden a nahiyar turai.
Gangamin wanda aka gudanar ranar litinin 23 ga watan janairu na shekarar 2023 ya biyo bayan wadansu mutane da suka kona Al’qurani mai girma a gaban ofishin jakadancin kasar Turkiyya dake birnin Stockholm na kasar ta Sweden.
Masu gangamin sun cika tituna a arewa maso gabashin birnin Sa’ada domin nuna bacin ran su dangane da wannan lamari kuma su bayyana damuwar su dangane da yadda wasu kasashen larabawa sukayi shiru kan lamarin.
Masu gangamin sun kuma rera baitocin “Alqurani yana da magoya baya” “Azzalumai zasu wulakanta” “Kona Al’qurani aikin azzalumai ne” “Makiya Allah sun kona Al’qurani” “Kira ga musulmi su hade kai, su daina tsoron makiya” da dai sauran su.
Shima gwamnan Lardin Sa’ada Mohammed Jaber Awad, ya bayyana kona Alqurani a Sweden matsayin abinda ya sabawa dokoki a lokacin da yake bayani ga mahalarta gangamin
Jaber Jawad ya bayyana, cewa wannan lamari yana faruwa ne a dai dai lokacin da kin jinin musulunci da musulmi ke kara kamari a nahiyar turai, wanda wasu ‘yan siyasa ke amfani da hanyoyin kara yadawa.
Gwamnan ya dora gabadayan laifin wannan abin takaici kan gwamnatin Sweden kuma ya bukaci musulmin duniya da masu neman ‘yanci da su bayyana kan kwalta domin nuna bakin cikin su dangane da wannan lamari.
Ya kuma bayyana wannan aiki matsayin babban abin takaici kuma ya bukaci ayi kwakwkwaran binciken dangane a kai.
Gidan jaridar Press T.v sun tabbatar da cewa dai Rasmus Paludan wanda shine shugaban Stram Kurs (Hard Line) Party ne ya kona kwafin Al’quranin ranar asabar kuma ya aikata hakan ne cikin bada kariyar ‘yan sanda tare da izinin gwamnati.
Al’ummara musulmi daga kasashe mabambanta sun bayyana takaicin su dangane da wannan abin takaici kuma sun tabbatar da cewa wannan ba ‘yancin fadin albarkacin baki bane illah cin zarafin musulmi ne akayi.