Rahotanni daga kasar Falasdinu na tabbatar da cewa a kalla fararen hula arba’in da biyar ne suka rasa rayukan su a sakamakon hare haren ta’addancin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta dingi kaddamarwa a kwanakin da suka gabata.
Kafar yada labarai ta Al-wafa ma ta rawaito cewa, Isra’ilan ta ruguje gidajen wasu firsunoni Falasdinawa guda biyu a yanzu ”west bank” wanda hakan yayi sanadin tagayyara mutane 14 gami da raba su da muhallan su.
Kamfanin yada labarai na Al-wafa ya bayyana cewa sojin Isra’ila sun dira a yankin kauyen Rummana dake arewa maso yammacin Jenin a safiyar ranar litinin kuma suka rushe gidajen firsunoni Yousef alRifai da kuma Subhi Imad Sbehat.
Wadannan mutane biyu ana tsare dasu a kurkukun Haramtacciyar Kasar Isra’ila tun watan Mayu bayan Haramtacciyar Kasar Isra’ilan ta zarge su da kokarin aiwatar da hari a gruruwan Bnei Brak da kuma Tel-aviv.
Kafin rushe rushe gidajen dai motocin jami’an sojin Isra’ila sun zagaye muhallin yayin da sojin Isra’ila ke tsare da wajen
A dalilin rushe rushe gidajen dai an bar mutum bakwai iyalan Yousef da kuma mutum bakwai iyalan alRifai ba tare da muhallin ba.
Tun da farko dai sojin Haramtacciyar Kasar Isra’ilan ne suka fara kame wani kwamandan Kungiyar Neman ‘yancin Falasdinu ta Jihadul Islamic, kafin daga baya su fara kaddamar da hare hare wanda suka fi shafar fararen hula raunana wadanda basu ki ba baau gani ba.
Gamayyar kungiyoyin jihadi masu rajin ‘yanto Falasdinawa fararen hula dai sun mayar da martani ta hanyar harba malamai masu linzami zuwa cikin haramtacciyar kasar Isra’ilan wanda ake da tabbatar zasu tafka ma kasar Isra’ilan babbar barna amma hukumomin haramtacciyar kasar Isra’ilan sunyi shiru dangane da wannan lamari.
Tashar Press Tv ta rawaito cewa Kungiyar Jihadul Islami ta amshi tayin tsagaita wuta domin samun zaman lafiya tattare da cewa tun farko sojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ne suka fara aukawa fararen hula larabawa.