A wani harin ba sani ba sabo da sojojin haramtaccciyar kasar isra’ila suka kai ranar juma’ar data gabata a kusa birnin nablus a dai dai inda ake cewa ”west bank” inda haramtacciyyar kasar isra’ila ta kwace daga hannun falasdinwa, harin ba sani ba sabon yayi sanadiyyar raunata falasdinawa a kalla dari hamsin.
Rikici dai ya barke ne yayin da sojoijin haramtacciyar kasar isra’ila suka kai hari kan gangamin nuna rashin amincewa da mamaye wani bangare mai suna jabil sabah da kuma aviatar inda haramtacciyar kasar isra’ilan take kokarin aiwatarwa.
Gangamin wanda ya aka soma bayan idar da sallar juma’a ya gamu da fushin sojojin haramtacciyar kasar isra’ila inda suka dingi harbin masu gangamin ga barkonon tsohuwa gami da harsasan roba..
Falasdinawa da dama sun ji munanan raunuka inda aka wuce da wasu daga cikin su asibiti yayin da sojojin na haramtacciyar kasar isra’ila ba tare da tausayi ba suka tsaya tsayin daka suka tabbatar da cewa falasdinawan ba zasu bayyana ra’ayin su ta hanyan gangamin lumana ba.
Kamar yadda kafar yaada labarai ta WAFA mallakin falesdin ta bayyana tace sojojin isra’ila sun dingi harba harsashin roba gami da gurneti kan masu gangamin wanda hakan yayi sanadin raunata akalla mutum dari da hamsin sakamakon garin.
Muhallin aviatar dake bangaren nablus ya zama sabon wajen da ake samun taho mu gama tsakanin sojojin haramtacciyar kasar isra’ila da kuma al’ummar falasdinu masu fafutukar neman ‘yancin kasar su daga hannun haramtacciyar kasar isra’ila.
Larabawan kasar falasdinu dai suna bukatar taimakon musulmi domin maganin matsalar data jima tana kawo cikas a lamurran rayuwan su wacce bata wuce barazanar haramtacciyar kasar isra’ila ba amma sai dai tare da wannan matsalar manyan kasashen larabawa irin su saudiyya da hadaddiyar daular larabawa sun bige da dasaw da gwamnatin haramtacciyar ksar ta isra’ila yayin da suka gaza neman ‘yancin raunanan falasdinawa daga hannun haramtacciyar kasar ta isra’ila.