Ministan harkikin wajen rasha ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da kafar sadarwa da Press T.v, inda minstan ya bayyana halin amurkan na satar dukiya a siriya a matsaya mummunan abu kuma wanda dokokin kasa da kasa basu amince dashi ba, inda ya tabbatar da cewa dole ne a kawo karshen wannan lamari da gaggawa.
Ministan harkokin wajen na kasar rasha, sergei lavrob ya bukaci amurkan data tsayar da kaka gidan da takeyi a kasar siriya domin babu dikar da ta bata damar shiga wata kasar kuma ta dinga daukan nauyin ta’addanci gami da samar da rashin tsaro domin amfana daga dukiyar da take a kasar.
Kasar rasha tana cikin manyan kasashen duniya wadanda suke takun saka da kasar ta amurka a bangarori da dama wanda a kwanakin bayan nan takun sakar ya tsananta duk da zama da shugabannin kasashen biyu sukayi amma kamar kwalliya bata biya kudin sabulu ba domin an shaidi karin habakar matsaloli tsakaninkasshen biyu.
Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnatin amurka tana kokarin tabbatar da cewa babu tsayayyiyar gwamnati a kasar ta siriya ne domin cigaba da dibar dukiya daga kasar ta siriya, lamarin da gwamnatin kasar karkashin jagorancin shugaba Bashar Al-assad bata amince dashi.
Bashar al-assad wanda ya cinye zaben da aka gudanar watan daya gabata yana samun goyon baya daga rasha da kuma jamhuriyar musulunci ta Iran inda a bangare guda amurka da saudiyya suka dauki matakin hada kai domin tabbatar da cewa gwamnatin ta bashar al-assad mai farin jinin al’ummar siriya bata kai labari ba.
Kasar ta siriya tasha fama da matsalolin ‘yan ta’addan ISIS kafin gwamnatin ta siriya tare da taimakon tsohon babban kwamandan sojin Iran Janaral Kasim Sulaimany ta samu nasarar kawo karshen matsalar ‘yan kungiyar wahabiyawan ISIS din wanda wannan kokari ya karawa gwamnatin mai ci ta Bashar al-assad farin jini a wajen mutanen siriya.
Babu tabbacin ko amurkan zatayi amfani da gargadin na rasha amma dai gwamnatin siriya ta tabbatar da cewa dole amurkan ta hanzarta barin kasar ta siriya.