Rahotanni daga jihar kanon najeriya na tabbatar da cewa zuwa yanzu shirye shirye sunyi nisa domin tabbatar da waye ke da gaskiya tsakanin babban malamin nan wanda ya assasa darikar kadiriyya riyadul jannah watau sheikh dakta abduljabbar muhammad nasir kabara da malaman maja, wadanda suka hada da wasu daga cikin darikun sufaye da kuma wahabiyawa.
Domin sanin halin da ake ciki mun shirya bayyana muku wasu muhimman batutuwa da suka shafi wannan gagarumar mukabala da aka jima ana jiran ranar da za’a gudanar da ita.
Daga cikin abubuwan da ya kamata al’umma su sani shine, a kwai sauye sauye da aka samu a yanayin gudanar da mukabalar ba kamar yadda aka tsara a baya ba.
Abu na farko shine kamar yadda labari yake ishe mu cewa, an hana ‘yan jarida yada zaman mukabalar kai tsaye wanda hakan kamar ya rage ma zaman mukabalar armashi ne domin maimakon mutane su san halin da ake ciki daga gidajen su yanzu babu wannan damar kuma kamar yadda masu sanya ido a lamurran suka ambata cewa idan ma an shirya rashin gaskiya a mukabalar zaiyi ma al’umma wahalar ganowa.
Abu na biyu daga ciki shine, hana almajiran malam abduljabbar su naji zaman mukabalar domin tabbatar da hujja wanda wannan ma ake ganin kamar wata makarkashiya ce ta hana bullar sahihan bayanai dangane da mukabalar.
Abu na uku daga ciki wanda atun farko ya zama kanun labarai shine yadda lokaci daya aka canja muhallin gudanar da mukabalar daga gidan sarki kamar yadda aka tsara zuwa ma’aikatar shari’a wanda wannan ma ana ganin kamar wata makarkashiya ce ta tabbatar da an tauye hakkin shehin malamin.
Wani babban abin lura dangane da wannan mukabala shine shehin malamin bai san da suwa zai tattauna ba sai da ya halarci wajen wanda hakan ya sabawa ka’idojin mukabala din.
Koma dai menene ana fatan mukabalar ta yiwu cikin nasara kuma gaskiya tayi halin ta.