‘Yan wasan jamhuriyar musulunci sun lallasa ‘yan wasan kasar wales, yayin da aka tashi Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta ci biyu, Wales kuma bata ci ko daya ba.
Wasan wanda ya dauki hankalin masu kallo sosai duba kan yadda ‘yan wasan Jamhuriyar Musulunci ta Iran din suka yi wasa mai kyau kuma suka dingi kai hare hare amma Allah bai sa sun ci kwallon ba sai a mintuna biyu na karshe.
Duban yadda ‘yan wasan Iran din sukayi wasa mai kyau Iraniyawa sun nuna murna gami jin dadin su kan wannan babban abin farin ciki.
Idan ba’a mance na Iran ta tashi 2-6 a karon ta da Ingila amma sai dai a wannan karon ‘yan wasan Iraniyawan sun nuna wannan karon a shirye suke.
Bayan fafatawa, kai hare hare masu yawa Iraniyawa sunyi nasara kan wales.
A ‘yan kwanakin baya dai Iraniyawan sun fuskanci matsin lamba daga kasashen turai a kan wani bakon lamari na dan hatsaniya wacce ta faru a Iran din wanda ake ganin yayi tasiri bisa ‘yan wasan Iran din a wasan Iran – Ingila.
Nasarar Iraniyawan a wannan wasan na nuna sun warware matsalar su kuma a wasannin gaba zasu iya lallasa duk ‘yan wasan kasar da suka gamu dasu.
Ana iya cewa ‘yan wasan Iran sun dawo filin wasa da karfin gaske bayan wasan su da Ingila, wanda hakan ke nuna akwai yiwuwar su taka rawar gani a wasannin su na gaba a kakar cin kofin duniya na bana, 2022.
Zuwa awanni ne dai za’a kara tsakanin Amurka da Ingila wadanda duk suna group din Iran din.
Zuwa yanzu Jamhuriyar Musulunci ta Iran itace ta biyu a jadawalin group din wanda hakan ke nuna babbar alamar da take tabbatar da Iran din zata fito daga group din.
Wasan Jamhuriyar Musulunci ta Iran zai kasance ta Amurka ne.