Jam’iyyar PDP ta zargi gwamnatin Buhari da zuga karya wajen fadin ayyukan da ta tayi a yayin cika shekaru shida bisa karagar mulki.
PDP ta bukaci gwamnatin Buhari da ta fito karara ta ce wa ‘yan Najeriya cewa ta gaza komai.
Hakazalika ‘yan Najeriya sun yi sharhi game da ci gaban da gwamnatin Buhari ke ikirari Aranar Asabar 29 ga Mayu, 2021 Shugaba Buhari ke cika shekaru biyu a wa’adin mulkinsa na biyu, a hade shekaru shida bayan hawansa mulki a 2015.
Jam’iyyar PDP ta bukaci shugaba Buhari da ya yi amfani da jawabinsa na ranar wajen amsa wa ’yan Najeriya cewa gwamnatinsa ta gaza, sabanin jawabansa na baya da ta ce suke ikirarin samun nasarorin bogi a yayin cika shekarun.
Sakataren yada labarai na PDP, Kola Ologbondiyan, ya kuma soki jam’iyyar APC mai mulki bisa zargin neman yi wa ’yan Najeriya ikirarin samun nasarori na bogi, alhali babu wata nasarar azo-a-gani da gwamnatin APC ta yi ko ta kammala a tsawon shekaru shida da take mulki.
Idan da gaske ne Fadar Shugaban Kasa da APC na da wata nasara da za su nuna, to mene ne na shirya gangamin wayar da kai ne don neman fahimtar ’yan Najeriya kan gazawarta.
Abin da ya kamata shi ne ayyukansu su yi magana da kansu kamar na gwamnatin PDP wanda har yanzu ake gani a kowane bangare na rayuwa a kasar nan.
“Idan suna abin da za su nuna, shin Shugaba Buhari zai rika rokon cewa ya kamata tarihi ya yi masa adalci a kan gazawarsa? Shin zai je Paris a kasar Faransa yana cewa gwamnatinsa ta yi rashin sa’a? “Jam’iyyarmu da kakkausar murya, tana watsi da yunkurin APC na ikirarin cewa gwamnatinta ta gaza ne saboda kalubalen da ya dabaibaye al’ummarmu.
A zahiri, kamata ya yi APC da gwamnatin Buhari su dauki alhakin gazawarsu.”
“Gwamnatin Buhari a 6: Ko makaho na iya ganin wasu abubuwa…” Yana mai nuni da irin ayyuka da ci gaba da gwamnatin shugaba Buhari ta kawo cikin shekaru shida kacal.
‘Yan Najeriya a nasu bangaren sun yi sharhi kan cikar gwamnatin shugaba Buhari shekaru shida, inda wani @Cooldemoore yake cewa: “Mista Femi, ina rokon rayuwarka ta shaida irin ci gaban da ‘yan Najeriya ke gani a cikin shekaru 6 da suka gabata kamar yadda ka yi ikirari. Aameen.”
@boyoarmani13 yace: “!Banda karya Mr Femi duk muna iya ganin ta’addancin, satar mutane, tayar da kayar baya, rashin bin doka da oda, rashin hukuntawa, hauhawar farashin kayayyaki kuma sama da komai ga rashawa da akeyi a wannan gwamnatin a cikin shekaru 6 da suka gabata.
“A madadin jama’ar Najeriya, Muna cewa mun gode. “Lallai muna iya gani. A wani labarin daban, Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa kasar na cikin aminci a hannun shugaba Buhari duk da kalubalen tsaro da ta ke fuskanta, The Punch ta ruwaito.
Ya shawarci ‘yan kasa da kada su yarda da mummunan hasashe game da Najeriya saboda ba za su zo ba.
Ministan ya fadi haka ne lokacin da ya karbi bakuncin Oluyin na Iyin-Ekiti, Oba Adeola Adeniyi Ajakaiye da mukarrabansa a ofishinsa da ke Abuja ranar Alhamis.