Shugaba muhammadu buhari a daren jiya ya bukaci jami’an tsaron najeriya da suka hada da sojoji ‘yan sanda da kuma jami’an farin kaya da su gaggauta daukan matakin gaggawa domin ceto rayuwar daliban da aka sace.
Shugaba buhari ya bayar da sanarwar ne a ta bakin mai bashi shawara kan lamuran yada labarai watau garba shehu, inda ya bayyana satar daliban a matsayin babban abin takaici kuma ba zai huta ba har sai an tabbatar da dawo da daliban gaban iyayen su tukuna,
Garba shehu ya bayyana matukara damuwar da buhari yayi danagen da hare haren da aka kai jihohin kaduna da nijer ina aka tafi da wani adadi na dalibai ‘yan makaranta.
Kamen dalibai ‘yan makaranta wani salo ne da aka shigo dashi domin karya lagon koyo da kowarwa a arewacin najeriya wanda hakan zai haifar da yawaitar wadanda basuyi karau ba a bangaren arewacin najeriya, hakan kuma zai ciyar da yankin baya sosai da sosan gaske kamar yadda wani mai sanya ido gami da sharhi kan lamurran arewa ya bayyanawa wakilan mu.
An dai tabbatar da cewa gwamnatin shugaba buhari bata wani babban kokari domin kawo karshen wannan matsala illah taron manema labarai da shan alwashin kawo karshen matsalar ta garkuma da mutane amma a kasa babu wani kokari za’a iya bayyanawa a ce gashi gwamnati tayi kokari domin kawo karshen matsalar.
A wani labarin na daban iyayen yaran da aka sace a kaduna sun yima na kusa da gwamnan jihar nasir el-rufa’i, samuel aruwan ihu gami da a ture yayin da ya kai musu ziyara.
Su dai fusatattun iyayen yaran sun zargi gwamnatin nasir el-rufa’i da yin halin ko in kula da rayuwar ‘ya’yan su saboda haka babu bukatar na kusa da gwamnan yazo musu jajejn munafurci.
A wani faifan bidiyo da aka wallafa a kafafen sada zumunta an nuna motocin samuel aruwan dole sukayi ribas suka koma ba shiri.