Rahotanni daga borno jihar maiduguri a najeriya na tabbatar da cewa kungiyar boko haram gami da harin gwuiwar ISWAP sun fara nada gwamnoni a wasu yankuna na jihar ta maidugu, wanda hakan yake karyata ikirarin cewa an cimma kungiyar kuma an gama da ita.
Bangaren boko haram da ISWAP din wadanda suke karbi jagoranci dan muhammad yusuf wanda ya assasa kungiyar ta boko haram ma’ana Al-barnawy sun tabbatar da fara nadin gwamnoni a wasu yankuna da sukayi ikirarin suna karkashin gwamnatin musulunci wacce suka kafa.
Baya bayan nan dai an jiyo gwamnan jihar ta maiduguri farfesa zulum yana cewa baya tsoron shiga kowanne lungu da sako na jihar ta maiduguri a halin yanzu.
Gwamnatin shugaba buhari tayi ikarari ganin bayan boko haram i8nda ta tabbatar da kashe shekau shugaban na boko haram mafi sanuwa a tsakanin al’ummar arewacin najeriya amma sai dai ikirarin na gwamnatin buhari ya gamu da suka daga bangarori daban daban na al’umma inda akayi korafin cewa gwamnatin ta baba buhari ta sha yin ikirarin gamawa da boko haram ko kuma ta kashe shekau din amma daga baya sai ta bayyana ba haka bane.
Kungiyar boko haram dai ta jima da bayyana biyayyar ta ga wannan babbar kungiyar ta’addancin masu akidar wahabiyanci watau Daesh.
Kamar yadda rahotanni suka zo kungiyar ta fitar da sunayen gwamnoni gami da wasu masu manyan mukamai a garuruwa mabambanta a kasar tasu da suka sira da kilafar msulunci.
Daga cikin matakan da sabuwar gwamnatin kungiyar ta dauka sun hada da cire takunkumin yin su a tafkin chadi, sabanin korar mutane daga garuruwanm marte, Abadam da kuma kukawa da sukayi kuma suka hana su a yankin.
Daga yanzu mambobin kungiyar wahabiyawan zasu dinga karbar N5000 daga kowanne dan kasuwa inda zasu dinga karbar N2000 daga kowanne masunci duk a cikin sabbin dokokin da kungiyar ta ta’addanci mai akidun wahabiyanci ta sanar.