Bikin idin ghadeer wanda mabiya tafarkin iyalan gidan annabta ma’ana dai wadanda aka fi sani da ‘yan shi’a sukeyi duk shekara ranar sha takwas ga watan zulhijja, menene asalin wannan bikin na ‘yan shi’a a tarihin musulunci, me yasa ‘yan shi’a ke gudanar da wannan bikin duk shekara, shin ma menene yasa ‘yan shi’ar suka muhimmantar da wannan rana ta ghadeer.
Tarihi littafan sunna da shi’a sun tabbatar da cewa a shekarar da manzon rahama (s.a.w.w) ya gabatar da hajin bankwana, ma’ana hajin da daga shi bai kuma gabatar da wani hajin ba kuma daga wannan hajin manzon Allah bai jima ba ya koma ga rahamar Allah ta’ala.
A wannan hajin malaman tarihi sun tabbatar da cewa manzon Allah yayi haji da akalla mutane sama da dubu dari da ashirin,
Bayan kammala hajjin a hanyar komawa gida ance a kwai wani tafki wanda yake kan mararrabar da ta hada hanyoyin yemen, misra, da kuma hanyar madina, dayar kuma ta koma makka.
A dai dai wannan wajen har sahabbai sun fara kama hanyar garuruwan su mabambanta amma manzon Allah (S.a.w.w) ya sa aka kirawo kowa da kowa ya dawo wannan mararraba da ake kira da ”Ghadeerkum” sa’annan ya sa aka tara masa siradan dawakai, ya hau ya kuma sa Imam Ali (S.A) shima ya hau sa’annan mazon rahama s.a.w.w ya kama hannun Imam Ali s.a ya daga sama yayi wannan shahararriyar hudubar tasa sa’annan yace ”Duk wanda na kasance shugaban sa, Ali ma shugaban sa ne”.
Tarihi ya tabbatar da cewa, dukkan sahabban da suke wannan muhalli a wannan lokaci sun shaidi hakan kuma ma manzon Allah s.a.w.w ya kallafa musu cewa ”Duk wanda ya samu sakon Ghadeerkum lallai ya isar dashi ga sauran mutane har zuwa ranar alkiyama”.
Wannan kenan, tarihi ya tabbatar da cewa sahabbai irin su umar da kaddabi da sauran su sun shaidi wannan wasicci na annabi s.a.w.w amma an kasa gane dalilin da yasa bayan wafatin annabi s.a.w.w aka canja kuma aka tozarta wasiyyar annabin rahama s.a.w.w.
Muna fatan Allah bamu taufiki ya ganar da al’ummar musulmi na duniya gabadaya kuma ya hada mu a kan wilayar Ali dan abi dalib r.a da ‘ya’yan sa tsarkaka jikokokin manzon rahama kuma diyan fadima s.a, albarkacin wannan rana ta bikin Ghadeerkum bikin da ya samu tarihi mai muhimmanci.