Kamar yadda kafar yada labari ta Yamen Almasirah ta rawaito babban sansanin sojin na amurka wanda yake a Al-omar a gabashin kasar siriya a gundumar Dayr Al Zawar ranar lahadin data gabata ya sha ruwan makamai masu linzami har guda biyu, al’amarin daya matukar tashin hankalin sojojin dake wannan sansani kuma ya sanya su cikin rudu gami da rashin tabbas.
Kafar sadarwa ta ”Russia Today” ma bangaren larabci ta jiyo Farhod wanda shine shugaban bangaren kungiyar nan masu ikirarin tabbatar da dimokoradiyya, wadanda ke samun goyon bayan amurka a kasar siriya wanda kuma suke dauke da makamai suna kai hare hare ya tabbatar da cewa makamai masu linzari guda biyu ne suka dira a sansanin sojin na amurka dake siriya.
Wasu rahotanni kuma sun tabbatar da cewa fashe fashen sun faru ne sakamakon bada horo da ake ma wasu sojoji ‘yan kasashen ketare wadanda amurka ta shigo dasu kasar ta siriya ba tare da amincewar gwamnatin kasar ta siriya ba.
Amurka ta tabbatar da sojojin kawancen ta a kasar siriya da kuma iraki a shekarar 2014 bisa ikirarin fada da kungiyar wahabiyancin nan mai kafirta musulmi ta ISIS.
Sai dai bincike ya tabbatar da cewa babban aikin sojojin kawancen amurka shine tabbatar da manufofin amurkan ne a kasashen na larabawa kuma tare da cewa gwamnatocin kasashen sun jima da tabbatar da rashin amicewar su da zaman sojojin na ketare a cikin kasashen nasu.
Amurka dai tana da sansanonin soji a yankin asiya a bangarori daban daban kuma tana amfani da wadannan sansanoni domin tabbatar da manufofin ta na siyasa da karfin soji kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
Amurka tana kokarin tabbatar da cewa bata fita daga kasar siriya da Iraki ba duk da cewa majalisun wakilan kasashen biyu sun jima da yanke hukuncin fitar amurka daga kasashen nasu amma amurkan tayi kunnen uwar shegu da hukuncin na majalisun wanda hakan ya saba ma dokokin kasa da kasa wanda amurkan ta sanya ma hannu, wanda hakan babban laifi ne a dokokin kasa da kasa.