Rahotanni daga kasar saudiyya na tabbatar da cewa auren misyar wanda yayi kama da auren mutu’a yana kara yaduwa cikin sauri a manyan garuruwa da kauyukan kasar wacce take kan tafarkin wahabiyanci kuma take fafutukar fada da shi’a wadanda suke zargi da halatta auran mutu’a.
Auran misyar ta janibi da dama yayi kama da auren mutu’a sai dai shi auren mutu’a ana ganin ‘yan shi’a sunfi gudanar dashi, amma a gefe guda an shaidi yaduwar auran misyar a tsakanin wahabiyan wadanda ke kasar ta saudiyya.
Kamar yadda kafar sadarwa ta The lawyer ta rawaito Auran misyar ya shahara da sunan auren babu matsawa kai domin babau bukatar namiji ya samar da kayayyaki masu tsada kuma babu ciyarwa babu bukatar yin gagarumin biki, abinda kawai wahabiyawan na saudiyya suke bukata shine tsakanin na miji da mace su daidaita junan su kan farashin da suka yadda dashi a matsayin ladan da namiji zai bama macen idan an kammala saduwa, amma babu maganar sadaki ko kuma abubuwan da addinin musulunci ya tanadar.
Ba bukatar samar da wurin zama balle ciyarwa a misyar hakan tasa da daman mutane suke ganin auran na misyar yayi kama da karuwanci domin kamar hakan zai bama masu bukatar iskanci da mata su samu saukin aiwatar da hakan bisa dogaro da cewa suna auren misyar ne kuma hukuma ba zata hukunta su bisa laifin zina ba sa’anna n al’umma zasu musu kallon ba ‘yan iska bane.
Majiyar mu ta tattauna da daruruwan ma’auratan misyar din amma sun tabbatar da cewa suna aiwatar da auran ne cikin sirii ba tare da sanin mutane duk da cewa gwamnatin kasar ta halatta auren ta hanyar malaman wahabiyyar kasar.
Gwamntin kasar ta saudiyya ta tabbatar da halaccin auran misyar ne domin yawaitar masha’a gami da zinace zinace da samar da ‘ya’yan shege a kasar.
Malaman saudiyya dai sun tabbatar da cewa an halatta auren misyar a kasar tun shekarar 1996 bisa fatawar babban muftin kasar na lokacin saboda haka saudiyyawa suna da damar kulla auren koda cikin sirii ne ba tare da shaidar mutane ba.