Gwamnatin amurrka karkashin jagorancin shugaba joe biden ta yanke shawarar sayarwa da daular saudiyya karkashin jagorancin Alu Sa’ud jiragen yaki kirar helikwafta wadanda kudin su ya kai a kalla dalar amurka miliyan dari biyar.
Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da duniya ke zargin amurka da taimakon kasar ta saudi arebiya wajen gudanar da ayyukan taaddanci a fadin duniya
Mai magana da yawun gidan gwamnatin amurka dai ne ya bada sanarwar inda ya tabbatar da cewa zuwa yanzu an cimma yarjejeniya har ma duk bangarorin sun sanya hannu kuma kasar amurka a shirye take domin tabbatar da wanzuwar wannan lamari.
Kasar saudi arebiya dai bata jima da firowa ta nemi yafiya dangane da kisan wannan babban dan jaridar jaml kashshogi ba wanda bisa umarnin yariman saudiyyan muhammad bin salman akayi masa kisan gilla a embassy din saudiyya dake istanbul babban birnin kasar turkiyya.
Ana dai kuma zargin kasar ta saudiyya da kisan kiyashi a kan al’ummar yemen, wanda wannan zargin yana gaban majalisar dinkin duniya ba’a kammala duba shi ba sai gashi kuma amurkan na shirin sayarwa da saudiyyar wadannan jirage wadanda kudin su ya kai dalar amurka har miliyan dubu dari biyar.
Idan har wannan ciniki da aka sawa hannu ya tabbata hakan zai bama saudiyyan damar cigaba da gudanar da ayyukan take hakkin dan adam, gami da laifukan yaki a fadin duniya musamman a kasar yemen wacce saudiyyan ke yima luguden wuta ba dare ba rana wanda abin ke shafar fararen hula wadanda basu ji ba basu gani ba.
Al’ummomi daga bangarori da dama ne dai musamman daga kasar yemen suke tir da wannan mataki da amurka ta dauka wanda ake ganin ya saba ka’ida, domin kamata yayi a sanyawa saudiyyan takunkuman tattalin arziki maimakon a shiga huldar sayar mata da makamai ba, hakan kamar kokarin bama saudiyyar dama ta cigaba da luguden wuta kana yemenawa.