Kamar yadda kafar sadarwa ta talabijin mai yada labarai da harshen ingilishi watau Press T.v ta wallafa a labaran ta na ranar juma’a 2 ga watan july shekara ta dubu biyu da ashirin da daya (2021), ya tabbatar da cewa amurka ta debe sojojin ta da kuma na kawancen NATO daga sansani mafi girma da take dashi a yankin bagram dake kasar ta afghanistan.
Amurka dai ta shiga kasar afghanistan fiye da shekaru ashirin da suka gabata da sunan yaki da ta’addanci bisa zargin shugaban kungiyar al’aida watau osama bin laden yana kasar inda amurkan ta shiga da sunan zata kamo shi amma tun wancan lokaci data shiga har zuwa yanzu bata kammala ita daga kasar ba.
Rahotanni sun tabbatar da cewa osama bin laden wanda shugaban babbar kungiyar ta’addancin nan ta wahabiyanci ne baya cikin kasar afghanistan sa’annan daga rahotanni suka tabbatar da cewa an kashe osama bin laden, har ma aka nuna hotunan gawar sa amma dai duk da hakan amurka bata ga yiwuwar fita daga kasar ta afghanistan mai yawan ma’adanai ba.
Sabuwar gwamnatin shugaba joe biden ce tayi alkawarin cewa lallai kasar ta amurka zata fice daga amuraka domin kawo karshrn abinda ta kira yaki mafi tsawo da kasar ta amerika ta shiga, inda shugaba joe biden ya tabbatar da cewa zai kawo karshen wannan yaki mai matukar tsawo wanda kuma yaci rayukan mutane da dama.
Kungiyar taliban wacce gurguzun masu akidar wahabiyanci ne na daga cikin babbar barazanar tsaro da kasar adghanistan take fuskanta.
A kwanakin baya aka shaidi hare haren rashin imani wanda kungiyar ta kai a kan wata makaranta wacce akasari yaran ‘yan shi’a ke karatu a ciki mai suna sayyidushshuhada inda kungiyar ta taliban tayi bombin din yarann ‘yan makaranta bayan an tashi daga karatu.
Kungiyar ta taliban ta dauki nauyin wannan hari kuma ta sha alwashin aiwatar da makamantan su indai ba’a biya musu bukatun da sujka zayyana ba.