A wallafa da tayi a shafin ta na tuwita aisha yusufu ta kalubalanci hukumar tsaron farin kaya ta najeriya cewa ya kamata ya zamana suna ma najeriya da ‘yan najeriya aiki ne ba wai jam’iyyar shugaban kasa da na kusa dashi kawai ba.
A wallafar ta ta aisha yusufu ta kalubalanci hukumomin tsaron najeriya dasuyi kokarin dakile matsalolin ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da neman kudin fansa gami da matsalar ‘yan boko haram da masu satar shanu.
A cewa aisha yusufu wadannan sune matsalolin da suke damu al’ummar najeriya amma hukumomin tsaron na najeriya sun bige da dukan taiki maimakon jaki.
aisha yusufu tana maida martani ne a wani wallafa da gidan jaridar sahara reporters suka wallafa a shafin su na tuwita inda suka bayyana cewa hukumar tsaron ta farin kaya ta tabbatar da kisan na kusa da sunday igoho kuma ta bukace shi daya bayyanar da kansa a ofishin ‘yan sanda mafi kusa.
Najeriya dai tana cikin kasashen yankin yammacin afirka da suke fama da matsalolin tabarbarewar tsaro wanda yake cin daruruwan rayuka a kowacce shekara kuma babbar bukatar ‘yan najeriyar shine gwamnatin shugaba buhari ta kaow karshen matsalar tsaron amma abin takaici kullum matsalar tsaron sai kata tabarabarewa takeyi.
Arewacin najeriya na cikin yankunan da suka fin fama da matsalar tsaro sakamakon mafiya yawancin kungiyoyin wahabiyanci masu tada kayar baya suna arewacin kasar.
A wani labarin na daban mambobin kungiyar rajin kafa kasar biyafara sun bukaci gwamnatin najeriya ta gaggauta sakin shugaban su inda suka suka bayyana kama shugaban nasu a matsayin wanda baya bisa ka’ida sa’annan kamar hakan yayi kama da take hakkin walwala da kundin tsarin mulkin najeriya ya bama kowa da kowa.
Shidai shugaban na masu rajin kafa kasar biyafara a kama shi ne da taimakon ‘yan sandan kasa da kasa watau interpol kuma ya jima da fadawa komar jami’an tsaron najeriya.