Tsohon shugaban kasar afirka ta kudu wanda ke jiran hukuncin kotu bisa laifukan da ake tuhumar sa dasu ya bayyana cewa shekarun sa sun haura tamanin sa’annan bisa la’akari da yaduwar cutar korona idan har kotu ta tura shi zaman fursuna zai wuta ya kai labari domin rayuwar sa zata zama cikin hadari daga kamuwa da annobar cutar korona.
A takardar koken da tsohon shugaban na afirka ta kudu ya shigar ranar juma’ar data gabata jacob zuma mai shekaru sama da tamanin ya bukaci kada kotu ta tura shi zaman fursina domin dalilan daya lissafa
Tun farko dai kotu ta bama tsohon shugaban wa’adin kwanaki ya sallama kansa ga jami’an tsaro amma har cikar wa’adin tsohon shugaban bai bayyanar da kansa ga jami’an tsaro abinda ya tilasta ma ‘yan sanda kama tsohon shugaban na afirka ta kudu kuma ake sa ran gurfanar dashi a gaban kuliya manta sabo a kwanaki masu zuwa.
Sai dai magoya bayan tsohon shugaban na afirka ta kudu a sassan kasar sun sha alwashin ba zasu taba bari a tunkuda keyar sa zuwa gidan yarin ba domin hakan ya saba da hankali a cewar su.
Mgoya bayan tsohon shugaba jacob zuman sun tabbatar da cewa matukar suna raye babu wanda ya isa ya tunkuda keyar tsohon shugaban na afirka ta kudu zuwa gidan yari.
Kamfanin yada labarai mallakin afrika ta kudu (SABC) ya tabbatar da cewa kotu ta amshi korafin tsohon shugaban kuma zata zauna domin yanke hukunci a kan yarda da rokon nasa ko kuma kin amincewa ranar sha biyu ga watan yulin wannan shekara ta 2021 da muke ciki.
Sai dai a bangare guda shugaban mabiya darikar shi’a na najeriya malam Ibrahim yaqoob zakzaky ya jima da shafe shekaru a gidan yarin tare da cewa ya haura shekaru tamanin a duniya kuma a kwai hadarin kamuwar sa da cutar ta korona amma mahukuntan najeriya basu dauki kowanne irin mataki domin kare lafiyar zakzakin ba.