Mohsen Isma’ili malamin jami’ar Tehran ya bayyana cewa, abu mafi muni da ya faru da zuriyar manzon Allah (SAW) na tozarci da kisan kiyashin da masu kiran kansu musulmi suka yi musu shi ne abu mafi muni da ya faru shekaru bayan wafatin manzon rahma.
Ya bayyana hakan ne a bayanin da yake gabatarwa wanda ake watsawa ta hanyar yanar gizo wanda masu bibiyar bayanan a cikin harshen farisanci sukan tarjama su zuwa wasu harsuna domin amfanin al’ummar musulmi.
A wani labarin na daban, Tashar TRT ta bayar da rahoton cewa, a cikin tsauraran matakan tsaro ne shugaban kasar Masar abdulfattah Al sisi ya halrci taron girmama sarakunan Fira’aunoni a birnin Alkahira.
A ranar ta jiya an fito da a kwatunan gawawwaki na sarakunan da aka yia kasar Masar dubban shekaru da suka gabata, domin dauke su daga wuraren da suke zuwa wani dakin ajiyar kayan tarihi sabo da aka gina.
Babbar manufar wannan abu ita ce kirkiro wata rana ta musamman domin tunawa da sarakunan da suka yi mulki da ake yi sarautarsu taken fir’ana dubban shekaru da suka gabata a kasar Masar.
To sai dai wasu daga cikin masana kan harkoki na addini na ganin wannan abu ya sabawa shari’a, domin kuwa littafan da aka saukar daga sama da suka yi bayani kan sarautar fir’auna, suna bayyana shi a matsayin mutum azzalumi.
Umar Ali, masani kan harkokin tarihi da kuma addinai, ya bayyana cewa; abin da Al sisi ya yi ya saba wa abin da yake a cikin addinin kirista da musulunci, domin kur’ani da Linjila duk sun ambaci Fir’auna a matsayin sarki masharranci, saboda haka girmama shi yana karo da abin da ke cikin wadannan littafai.
Tun lokacin tsohon shygaban kasar Masar Husni Mubarak ne ya nemi kirkiro wata rana makamanciyar haka, amma sakamakon sukar hakan da al’ummar Masar suka yi, ala tilas Husni Mubarak ya janye shirin nasa.