Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bukaci a kawo karshen yakin da ke faruwa a halin yanzu a kasar Habasha.
Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bukaci a kawo karshen yakin da ke faruwa a halin yanzu a kasar Habasha. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto kakakin babban sakataren Stephane Dujarric yana fadar haka a jiya Talata, ya kuma kara da cewa Guteress ya bukaci dukkan bangarorin da suke fafatawa da juna a kasar su dakatar da budewa juna wuta nan take, su kuma bawa ‘yan agaji masu aikin tallafawa majinyata su shiga yankunan da ake fafatawa a Lardin Tigray don taimakawa wadanda suka ji raunuka
Labarin ya yi kira da gwamnatin kasar Habasha ta kawo karshen hare-hare da jiragen sama wadanda take kaiwa kan yankin na Tigray don hare-haren suna shafan fararen hula da dama a yankin. Ta Kuma bude hanya don a isarda kayakin agaji ga mabukata.
A cikin watan nuwamban shekara ta 2020 ne gwamnatin Abiy Ahmed tare da zargin mayakan Tigray da kai hari kan sojojin kasar sojojinsa suka farwa yankin da yaki suka kuma kwace birnin Makelle babban birnin Lardin duk da cewa daga bayan mayakan na Tigray sun dawo da ikonsu a garin.