Shahararren malamin addinin musulunci kuma shugaban bangaren ‘yan uwa musulmi wadanda aka fi sani da ‘yan shi’a Sheikh Ibrahim Yaqoob Zakzaky a daren jiya talata ya shilla zuwa kasar Iran domin ganin likitoci.
Kamar yadda sanarwa da nuna malamin ya bayyana a wani bayani nasa kwanakin da suka wuce cewa, sun karbi fasfunan su kuma suna nan shi da mai dakin sa Malama Zinat suna shirye shirye saboda haka kowanne lokaci za’a iya jin sunyi tafiya.
Malamin na mabiya mazahabar shi’a wanda kokarin fitar sa kasashen ketare ya tayar da kura wacce ba’a saba ganin irin ta a kan tafiyar wani mutum ba wannan karon dai ya samu fita domin neman lafiya.
Idan ba’a mance ba a shekarar 2015 ne dai sojoji suka dira gidan malam Ibrahim Zakzaky dake unguwar gyallesu inda suka kashe almajiran jagoran ‘yan shi’an fiye da dari uku tare da raunata da dama ciki har da malamin da kuma mai dakin sa kuma suka kama malamin suka tafi da shi.
Daga bisani kotu ta wanke malamin kuma ta tabbatar da cewa ba shi da laifi a abinda aka tuhume shi inda bayan haka malamin yace yana bukatar fita kasashen ketare domin ganin likitoci amma sai dai takardun tafiyar sa dana mai dakin sa sunyi batan dabo.
Almajiran malamin sun zargi hukumar kula da shige da fice ta kasa ta rike takardun tafiyar malamin inda suka dingi jerin gwanon lumana a garuruwa mabambanta ciki har da babban birnin tarayyar Abuja.
Kwatsam sai malamin a wani jawabi nasa wanda ya gabatar ranar mauludin bana ya bayyana cewa anzo gida an dauki bayanan su kuma anyi musu fasfunan.
Ana sa ran malamin zai tafi kasar Iran domin neman
lafiya.