Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta yi gargadi a game da yadda ake samun karuwar wadanda ke kamuwa da cutar korona a Afirka, musamman ma lura da yadda ake samun nau’ukan cutar iri-iri a nahiyar.
Shugaban Sashen Gudanar da Ayyukan Gaggauwa na Hukumar ta WHO Michael Ryan wanda ke zantawa da manema labarai a birnin Geneva a wannan juma’a, ya ce yanayin cutar a Afirka na matukar tayar da da hankula.
A cewar alkaluman hukumar ta WHO, adadin wadanda suka kamu da cutar ya haura dubu 116 a cikin makon da ya gabata, wato dai an samu karin mutane dubu 25 da suka harbu da kwayar cutar a cikin mako daya.
Duk da wadannan alkalumma, har yanzu Afirka na matsayin nahiyar da aka fi samun karancin wadanda annobar ta Covid-19 ta yi wa illa, to amma duk da haka kawo yanzu ta kashe mutane dubu 136 daga cikin sama da milyan 5 da suka harbu da ita.
Hukumar ta lafiya ta bukaci kasashen duniya su kara azama domin wadatar da duniya da allurar rigakafin kariya daga wannan cuta, yayin da alkaluma ke nuni da cewa, adadin wadanda suka karbi zagaye na biyu na allurar har zuwa yanzu bai wuce 1% ba a Afirka.
Annobar cutar korona ba nahiyar afirka ba, Nahiyar turai ma tana tsaka da fama da ita, hasali ma babu inda cutar ta korona take cin karen ta babu babbaka a wannan lokaci irin kasashen nahiyar turai musamman amurka, italiya da kuma ingila wadanda suke da adadin miliyoyin wadanda suka kamu gami da wadanda suke mutu a sanadin annobar cutar ta korona biros.
Tare da wannan rahoho na yawaitar annobar cutar korona a nahiyar turai ko menene yasa hukumar kula da lafiya ta WHO ta zabi ta gargadi kasashen nahiyar afirka maimakon kasashen turai inda cutar tafi ta’azzara?