(WHO) Na Shirin Kafa Asibitoci A Sahara Biyo Bayan Mummunar Barna Da Hare-haren Da Isra’ila Ke Kai Wa Zirin Gaza.
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na – ABNA – ya habarta maku cewa: Richard Pepperkorn wakilin hukumar lafiya ta duniya a birnin Kudus da aka mamaye, ya sanar da cewa hukumar lafiya ta duniya (WHO) na shirin kafa asibitocin sahara a can biyo bayan mummunar barna da hare-haren da Isra’ila ke kai wa zirin Gaza.
A cewarsa, akwai gadaje asibiti kusan 3,500 kafin a fara yakin, amma a yau akwai gadaje 1,400. A halin da ake ciki, ana bukatar akalla gadaje 5,000 saboda barnar da aka samu da kuma jikkata da dama.
Baya ga wannan, dole ne a gaggauta kwashe mutane tsakanin 50 zuwa 60 da ke fama da munanan cututtuka daga zirin Gaza domin samun isasshen kulawa a Masar.
Peppercorn ya kuma yi gargadi game da yaduwar cututtuka daban-daban a zirin Gaza. “Mutane sun damu matuka,” in ji shi. Fiye da mutane 70,000 na kamuwa da cututtukan numfashi da kuma fiye da 44,000 na cutar gudawa wanda aka tabbatar da su a cikin yankunan bakin teku mai dauke da yawan jama’a.
Source: ABNAHAUSA