Abokai, a daren ranar 26 ga watan Disamban shekarar 2022 ne, gwamnatin kasar Sin ta ba da sanarwa , inda ya sauya sunan cutar huhu ta Coronovirus, zuwa cutar kwayar sabuwar Corona, kuma sanar da cewa, daga ranar 8 ga watan Janairu na sabuwar shekara, za ta fara aiwatar da dokar kandagarkin annobar bisa dokar Jamhuriyar jama’ar kasar Sin, inda za a rage matsayin cutar.
Daga waccan lokaci, ba za a killace masu kamuwa da cutar da wadanda suka yi alaka da su ba, kuma ba za a yiwa wadanda za su shiga kasar Sin gwaji da kayayyakin da suka shigo kasar ba.
Sin ta daidaita manufarta ta kandagarki saboda yadda kwayar cutar ta sauya daga Delta zuwa Omicron, babban aikin dake gabanta a yanzu shi ne tabbatar da lafiya da tsaron al’umma da hana kamuwa cutar.
A wani bangare kuma, manufar za ta ingiza farfadowar tattalin arziki da al’umma, da tabbatar da zamantakewar al’umma, matakin da zai taka rawa wajen farfado da tattalin arzikin duniya, wanda ya dade yana fuskantar koma baya.
Gwamnatin Sin ta daidaita manufarta ta kandagarki bisa muradun jama’a.
Ta zabi hanyar da ta dace da halin da kasar ke ciki, abin da ya bayyana niyyarta ta mai da moriyar jama’a a gaban kome da kula da rayukan jama’a, ban da wannan kuma ta taka rawa wajen farfado da tattalin arzikin duniya baki daya