Sarkin ya yi magana wajen taron yi wa tsarin mulki kwaskwarima a Kebbi, Sa’ad Abubakar III ya bukaci a kyale matan Musulmai su rika sa Hijabansu.
Sarkin Musulmi ya ce dole tsarin mulki ya ba Musulmai damar rike addini Mai alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III, ya na kiran a ba matan Musulmai damar sanya Hijabi ba tare da wata tsangwama a kasar nan ba.
Daily Trust ta ce Alhaji Sa’ad Abubakar III ya na neman a ba matan da suke musulunci wannan ‘yanci kamar yadda kowa yake da ikon yin ibadarsa.
A matsayinsa na shugaban majalisar kolin addinin Musulunci na Najeriya, Sultan ya bayyana wannan wajen sauraron gyara kundin tsarin mulki.
Jaridar The Cable ta ce an yi wannan zama ne a garin Birnin Kebbi a ranar 1 ga watan Yuni, 2021.
Sa’ad Abubakar III ya koka a kan abin da ya sa amfani da Hijabin da ake yi, ya zama matsala ga wasu wanda babu abin da ya hada su da musulunci.
Ya ce: “Muhimmin abu shi ne lamarin addini. Ubangiji ya halicce mu ne domin mu bauta masa, kuma dole a bani wannan dama a matsayin musulmi.”
“Dole ne a kare hakki na a matsayina na musulmi a kowane takarda za a kawo nan.” Inji Sultan.
“Dole ne a bani ‘yancin bautar Madaukakin Sarki yadda Allah yake so ayi masa ibada. Meyasa wasu suke surutu a kan maganar shari’a da dabbakata?” Mai alfarama ya ce:
“Na yi imani cewa babu wanda zai hana ni yin addini na, dole in yi bauta bakin karfi na, ba tare da na hana wasu suyi nasu addinin ba.”
Sultan ya ce Musulmai suke da akalla 50% na adadin mutane a Arewa, yamma, da kudancin kasar nan, amma a kan hana matansu sa Hijabi a wasu wurare.
A jiya ne ku ka ji cewa shugaban Majalisar dokokin jihar Kano ya ci amana, ya shigo Najeriya da takardun COVID-19 na bogi bayan ya kammala Umrah a Saudi.
Da farko an nemi a killace Hamisu Chidari, sai ya ce zai kebe a wani otel.
Ba a tabbatar ko ‘Dan siyasar bai warke da Coronavirus ba, sai ya sulale ya shiga jama’a.