Ma’aikatar lafiya a birnin Karbala na kasar Iraki ta ce an tura tawagogin likitoci sama da 100 da motocin daukar marasa lafiya 100 domin yi wa masu ziyarar Imam Husain As hidima a lokacin Arba’in.
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA – ya habarta cewa, Ma’aikatar lafiya ta birnin Karbala na kasar Iraki ta ce an tura tawaga sama da 100 na likitoci da motocin daukar marasa lafiya 100 domin yi wa maziyarta hidima a lokacin tarukan Arbaeen.
Sabah Al-Mousawi, shugaban sashen shi ya bayyana hakan da cewa, an jibge tawagogin likitocin da motocin daukar marasa lafiya a sassa daban-daban na birnin na Karbala da kuma kan hanyoyin da suka isa birnin mai alfarma.
Asibitoci takwas na gwamnati da kuma asibitoci masu zaman kansu da asibitocin filaye da aka kafa a kan hanyar Najaf zuwa Karbala suma a shirye suke don ba da ayyukan jinya da lafiya ga maziyartan, in ji shi.
A cewar jami’in, kungiyoyin lafiya 55 ne za su kula da rabon ruwa da abinci ga Masu Ziyarar domin tabbatar da cewa suna cikin koshin lafiya.
Al-Mousawi ya ci gaba da cewa, akwai matakai na musamman na hana yaduwar cututtuka a tsakanin maziyartan a lokacin tarukan Arba’in.
Ranar Arbain ita ce cikar kwanaki 40 bayan Ashura, ranar shahadar jikan Manzon Allah SAW, Imam Husaini (AS). Arbaeen na bana zai fado ne a ranar 6 ga Satumba.
A kowace shekara, dimbin mabiya Shi’a ne ke tururuwa zuwa birnin Karbala, inda hubbaren Imam Husaini (AS) yake, domin gudanar da zaman makoki.
Maziyartan dai sun fito ne daga kasashen Iraki da Iran da Sauran Kasashen du iya gaba daya, suna tafiya ne daga dogayen hanyoyi da kafa zuwa birnin mai alfarma.
Source: LEADERSHIPHAUSA
A farkon wannan wata ne jami’an kasar Iraki suka bayyana shirinsu na karbar bakuncin maziyarta miliyan biyar daga kasashe daban-daban a lokacin tarukan Arba’in.