An yi gargadin cewa sama da mutum miliyan daya na fama da yunwa a kudancin Madagascar saboda mummunan farin da ake fuskanta cikin sama da shekara 40.
Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International, ta ce ya kai ya kawo mutane sama da dubunnai na cin ciyawa a yankin domin su rayu.
Kuma mutane suna sayar da abin da suka mallaka domin su aika yaransu wajen aiki su sau kudin da za su sayi abinci da shi.
Wata mata mai sama da shekara 63 da ke da jikoki tara ta bayyana yadda iyalanta ke cin abinci sau daya a rana – wataran su ci rogo a matsayin abincin dare.
“Muna cin ciyawa masu kaya a wasu lokutan da safe, a wasu lokutan har kuka nake idan naga yaran suna ci, amma ba zan iya komai ba akai,” in ji Oline Ampisoa.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce duka kauyukan wajen babu komi a cikinsu saboda haka mutane ke guduwa wasu wuraren domin tsira.
A wani labarin na daban Kungiyar gwamnonin kudancin Najeriya ta ce matakin haramta kiwon sake a yankin babu gudu ba ja-da baya kuma za su tabbatar da aiki da mataki.
Wata sanarwa daga gwamnan jihar Ondo, shugaban Ƙungiyar gwamnonin ya ce za su bi dukkan hanyoyin shari’ah don tabbatar da ganin sun aiwatar da manufar hana kiwon.
Wannan dai na zuwa ne bayan Ministan Shari’ar ƙasar Abubakar Malami ya soki matakin, inda ya kwatanta shi da cewa tamkar hana sayar da kayan gyaran mota ne a arewacin Nijeriya.
Cikin sanarwar kungiyar gwamnonin kudancin Najeriya ta ce babu ja babu gudu da baya a wannan mataki da suka dauka.
A don haka sai dai su hadu da Ministan na Shari’a a kotu matukar ya dage kan cewa matsayar ta su haramtacciya ce.
A ranar Laraba ne Ministan Shari’ar Ministan ya ce babu wani dan Najeriya da ke da yancin hana wani yawo a kasar tare da dukiyarsa, a wata hira da gidan talabijin na Channels a Najeriya.