Ana zargin wani likita a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano (AKTH) daa sakacin illata wani jariri dan kwana biyar a duniya.
Likitan dai ya bar tsirkiyar da ya daure hannun jariri da ita yayin daukar jini har tsawon awanni 18.
Wannan sakacin ne ya jawo hannun yaro ke neman rubewa a halin yanzu.
A binciken da wakilin gidan rediyon Premier FM ya gabatar, ya gano cewa an yi wa mahaifiyar yaron aiki ne aka ciro shi daga cikinta.
Daga bisani likitan, ya ce yana fama da matsalar numfashi, wanda hakan ya sa tilas aka kwantar da shi a bangaren jarirai.
Tuni dai wasu likitoci suka ce sai dai a yanke hannun wannan jariri, sakamakon shafe tsahon lokaci jini bai gudana ta hannun ba.
Sai dai mahaifin yaron, Malam Umaru Shamsu, ya ce ma’aikatan asibitin na nuna masa wulakanci duk da dattakon da ya nuna.
Ya ce, ya yi mamaki da aka kira shi wai ya je ya sayo maganin da za a bai wa dan nasa a ranar Litinin, duk da danyen aikin da aka yi masa.