Zaka ga wani har wani takama yake shi yana iya rike fitsari zuwa tsawon lokaci, kuma sai lokacin da ya ga dama yake yi.
Masana lafiya sun magantu kan irin wannan dabi’ar sannan kuma sun fadi illar da ahakn ke haifarwa.
In mutum bai yi wasa ba ya kan iya rasa rayuwarsa sabida rike fitsari ba tare da yayi shi akan lokaci ba.
Masana lafiya sunce yunkuri ko kokarin da mutane suke na rike fitsari tsawon lokaci, na kawo cutar koda duk da binciken masana lafiya bai ka ga wajen ba har yanzu a kimiyance. inji masanin, sun ce to har yanzu dai a kimiyance, ba’a samu wani bincike da ya tabbatr da wannan batun, amma akwai kanshin gaskiya a batun.
Yayin da yake magana da gidan jaridar The Punch, wani kwararren mai kula da mafitsara Dr Babawale Bello shi da wani abokin aikinsa Aliyu Sokoma yace akwai batu kan rike fitsari na kawo ko janyo cutar koda.
A Jikin Dan Adam
Bello wanda yake kwararen likitan koda ne, da yake aiki asibitin koyarwa na Lagos, yace mai yiwuwa ne ne cewa rike shi ko kuma yanayin yinsa yadda aka ga dama kan iya kawo cutar koda.
Gaskiyar ikirarin Yace cutar kodar da ake tunanin za’a iya samu daga rike fitsari itace wadda take a cikin kwararon jijiyar da take fitar da ruwan fitsarin zuwa mafitsara.
Yace jijiyar mafitsara kan iya tushewa indai an rike fitsari, wanda hakan kan sa a samu cuta a jikin jijiyar wadda zata iya janyo cutar kodar.
Yace wannan batun na toshewar mafitsara bincike ya tabbatar da ba wai iya rike fitsari bane yake janyo ttoshewarsa ba akwai sauran abubuwan da suke da alaka da wasu cuttuttukan.
Alamun cutar koda Masana lafiyan sunce alamun cutar koda ba’a iya ganinsa har sai ya ta’azzara, alokacin da mutum ya fara ji a jikinsa, a dalilin haka suke kira da mutane suje su ringa duba lafiyarsu akai-akai, musamman ma wanda suke da cutar Sikari, Hawan jini ko cutar kanjamau.
Akwai bukatar wanda yaji wasu alamu da bai saba jin sa a jikinsu ba da ya garzaya asibiti mafi kusa da shi domin a duba lafiyarsa.