Akwai sauyin da ake samu na yadda mutane ke cin abinci ya sa ana samun karuwar masu cutar a kasar Najeriya , inda matsalar ta fi yawa a biranen Kano da Legas, jihohin da suka fi yawan al’umma.
Masana a fannin kiwon lafiya sun bayyana cewa kauracewa abincin gargajiya zuwa wasu nau’oi’n abinci na turawa shi ma yana taimaka wajen samun karuwar masu ciwon sikari.
Hukumar lafiya ta duniya, WHO, ta bayyana cewa mutane miliyan 422 ne suke fama da wannan cuta a fadin duniya.
Haka nan kuma masu fama da wannan larura sun fi yawa ne a kasashe masu matsakaici da kuma karancin kudaden shiga.
Hukumar ta kara da cewa akalla mutane miliyan 1.600,000, ne suke mutuwa duk shekara a sanadiyyar cutar, wannan al’amarin ne ya sa cuta ta zama daya daga cikin manyan cututtukan da suke sanadiyar mutuwar mutane a fadin duniya.
Hukumar ta kuma bayyana cewa, cutar nau’i biyu ce, akwai wadda jikin mutum baya iya fitar da wani sinadari da ake kira ‘Insulin’ ko kuma yana fitar da kalilan ne, idan ma yana iya fitarwa.
Nau’i na biyu kuma; na ciwon, shi kuma sinadarin na Insulin ba ya wani yin tasiri a jiki.
Kuma wannan nau’i na biyu kamar yadda hukumar ta bayyana, shi ne wanda ya fi yawa a duniya, musamman ma a tsakanin manya.
A wani labarin na daban, kusan mutane dari da hamsin sun rasa rayukan su a sakamakon hadarin jirgin ruwa daya faru a jihar kebbin Najeriya.
Kamar yadda kafar sadarwa ta Press TV ta rawaito jirgin ruwan yayi hadari ne inda wannan adadi suka rasa rayukan su a yayin da da dama kuma suka ji raunuka kuma suke karkashin kulawar taimakon gaggawa domin ceto rayukan su.
Zuwa yanzu dai bamu ji ta bakin gwamnatin jihar ta kebbi ba dangane da faruwar al’amarin, sai dai ana sa ran samun cikakken rahoto da zarar mun ji ta bakin gwamnatin jihar kebbin ta Najeriya ba.