An tunasar da ‘yan Nijeriya masu amfani da Taliyar Indomie da su sani cewa ana sarrafa ta ce a kasar nan ba wai ana shigo da ita daga kasar waje ba, haka kuma sinadaran da ake yin amfani da su wajen sarrafa ta na ethylene oxide ba a Nijeriya ake samar da shi ba. (NAFDAC)
Duk da cewa, Taliyar ta Instant Noodles, na daga cikin haramttauun kayan da aka haramta shigo da su cikin kasar nan, an shawarci masu yin amfani da wacce ake sarrafawa a Nijeriya da su saye ta su kuma yi amfani da ita.
Akwai fargaba ga wasu ‘yan Nijeriya ganin cewa ana magana a kan Taliyar ta instant Noodles a faɗin duniya a halin yanzu.
Da an yi maganar Taliyar ta noodles kawai ana ɗaukar Taliyar Indomie ake nufi.
Wannan na faruwa ne ganin cewa Indomie na a kan gaba a kasuwar da ta yi a fadin duniya a fannin sarrafa noodles.
Hakazalika, wannan matsayin ya zo ne daidai lokacin da ake son inganta Taliyar da rabar da ita.
A 2022, wani rahoto da aka fitar a kasuwar da ke a Gabashi da Kudancin Afirka da aka wallafa a kafar yanar Gizo wato (COMESA) an gargaɗi ‘yan Kasar Masar kan su guji cin wasu nau’uka na Taliyar Indomie Instant Noodles saboda zargin tana dauke da wasu nasadarai da za su iya shafar kiwon lafiyarsu.
Kamar a yankin Larabawa, fargaba ta ci gaba da yaduwa a kasashen da ke makwabta da iyakokin Masar.
Hakazalika, a Nijeriya wasu kafafen yaɗa labara sun ci gaba da wallafa rahoton da ya fito daga Masa.
Inda suka ci gaba da jefa tsoro a zukatan ‘yan Nijeriya, inda hakan ya sa Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasa NAFDAC da Hukumar kula da ingancin sarrafa kaya ta ƙasa (SON) suka shigo cikin lamarin tare da tsunduma kan yin aiki game da maganar guraɓatacciyar Taliyar da ake shigowa da ita cikin ƙasar nan ta hanyar fasa-ƙwaurin ta.
A ƙarshen bincike, an gano cewa, ba a saɓa ka’idar iyaka ba wajen shigo da ita kuma kasuwanninmu ba su fuskantar wata barazana.
An gano sanadarin na ethylene oxide a cikin Indomie na janyo cutar daji, a kasashen Taiwan, Malaysiya, inda bayanin da jami’an kiwon lafiyar kasashen suka yi ya haifar da raɗe-raɗi da jefa tsoro a cikin zukatan ‘yan Nijeriya.
Kafafen yada labara sun ci gaba da ƙara gishiri a miya tare da yin kanun labarai masu zafi don jefa fargaba a zukatan jama’a.
Kamfanin sarrafa taliyar ta Indomie a Taiwan da Malaysia da kuma kamfanin Dufil Prima Food Plc da ke a Nijeriya da ke sarrafa Indomie Instant Noodles a cikin kasar nan su ma an tantance su don guje wa kalubalen na cikin gida.
A hirarta da manema labarai, Darakta Janar ta NAFDAC, Mojisola Adeyeye ta sanar da cewa, Taliyar ta Instant noodles, na daga cikin kayan da gwamnatin tarayya ta haramta shigowa da su cikin kasar nan, inda ta ce, ita Taliyar da ake magana a kai hukumar ba ta yi mata rijista ba kuma sannan ba a Nijeriya ake sarrafa ta ba.
Ta ce muna yin takatsantsan don ganin ba a yi fasa-kwauarin ta zuwa cikin Nijeriya ba.
Shugaba sashen sadarwa da shirya tarurruka na kamfanin Dufil Prima Foods Plc, Tope Ashiwaju, ya bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin cewa, ɗaukacin nau’o’in Taliayarta Indomie Instant Noodles a cikin kasar nan ake sarrafa su kuma bisa doka da oda.
“Muna bin ƙa’idar inganci sau da ƙafa da Hukumar NAFDAC da Hukumar Kula da Ingancin Kayayyaki ta Ƙasa (SON) suka shimfiɗa a dukkan kamfanonin sarrafa kayanmu. Muna amfani ne kawai da kaya masu inganci da ake samarwa daga sahihan masu kawo kaya kuma ana duba na’urorin da muke aiki da su a kai a kai tare da tantance su domin tabbatar da cewa suna da ingancin da ya kamata.” In ji shi.
Source:LeadershipHausa