‘Yan-sandan Holland sun ce sun sami wani mutum da ya makale a tayar jirgin sama wanda ya tashi tun daga Afirca ta Kudu ya sauka a Amsterdam a raye.
Jiragen sama na tafiyar sa’a 11 daga Johannesburg zuwa Amsterdam, kuma wannan jirgin na dakon kaya ana ganin ya yada zango ne sau daya kawai a Nairobi, Kenya.
Abu ne mai wuyar gaske ga mutumin da ya makale a tayar jirgin sama ya rayu a doguwar tafiya, saboda tsananin sanyi da kuma karancin iskar shaka a can sama