Kawo yanzu an tabbatar da mutuwar mutane 11 bayan da wani matashi mai suna Shafi’u Abubakar ya yi kwantan ɓauna ya cinnawa wasu masallata wuta lokacin da suke tsaka da yin sallar Asuba a garin Gadan da ke ƙaramar hukumar Gazawa.
Kawo yanzu an tabbatar da mutuwar mutane 11 bayan da wani matashi mai suna Shafi’u Abubakar ya yi kwantan ɓauna ya cinnawa wasu masallata wuta lokacin da suke tsaka da yin sallar Asuba a garin Gadan da ke ƙaramar hukumar Gazawa
Iftila’in dai ya faru ne a jiya Laraba, in da Matashin mai shekaru 38, ya ce ya yi hakan ne sakamakon fushin rikicin rabon gado, bayan ya cimma wutar ne ya kuma kulle ƙofar masallacin don kar wani ya samu damar ficewa.
An dai ruwaito cewa lokacin da lamarin ya afku akwai kimanin mutane 40 da suke sallar Asuba a cikin masallacin, bayan samun damar fitar da su ne aka garzaya asibiti domin duba lafiyarsu, sai dai kash 11 daga cikinsu sun riga mu tafiya gidan gaskiya.
Wani mazaunin garin mai suna Rabi’u Gadan ya shaidawa LEADERSHIP Hausa cewa; tuni dai har an gudanar da jana’izar 8 daga cikinsu Kuma na shirye-shiryen yinta ragowar ukun. Rabi’u ya ce harin masallacin ba wannan ne ta’addacin da matashi Shafi’u ya taɓa yi ba a ƙauyen nasu, domin ya taɓa yi wa yayanninsa biyu rutse kuma ya kai kansa wurin ƴan sanda ya ce wai ya kashe su.
Wani mazaunin garin mai suna Malam Garba ya ce; Da ma can matashin fitinanne ne don har an taɓa kai shi gidan asibitin masu motsin ƙwaƙwalwa amma likita suka ce lafiyarsa ƙalau, kuma a lokacin da ya ƙalubalanci danginsa da cewa lallai sai sun ba shi rabon gadonsa, sai ku raba suka ba shi. Don haka lafiyarsa kalau ya cinna wutar, kuma biyu daga cikin waɗanda suka rasu kawunnansa ne.
DUBA NAN: Daliba Ta Nemi Makarantar Su Ta Biyawa Tarar Naira Miliyan 550 A Kotu
Shi dai wannan matashi yanzu haka yana can tsare a hannun jami’an tsaro ana cigaba da bincike.