Abbas Balarabe, ya yanke jiki ya fadi a lokacin da majalisar dattawa ke tantance shi a gaban kwamitin tantance wadanda za su zama minista.
Balarabe dai ya kammala karanta takaitaccen tarihinsa, yayin da majalisar dattawa ta dage zamanta zuwa karfe 2 na rana, lokacin da lamarin ya faru.
A ranar Talata ne Shugaba Tinubu ya zabi Abbas a matsayin wanda zai maye gurbin El-Rufai daga jihar Kaduna a matsayin minista.
Idan ba a manta ba, majalisar dattawa ta ki tantance tsohon gwamnan Kaduna, kan rahoton tsaro da DSS suka bayar a kansa.
Rashin tantance El-Rufai ya bar baya da kura tare da haifar da zazzafar muhawara a tsakanin ‘yan Nijeriya.
Wasu na ganin tsohon gwamnan na da kwarewar da ya kamata ya zama daya daga cikin jerin ministocin gwamnatin Shugaba Tinubu duk da rahoton da aka bayyana a game da shi.
A gefe guda kuwa wasu na ganin tsohon gwamnan na Kaduna, ya yi wasu kalamai masu tsauri da suke da alaka da tsaro wanda ake ganin su ne dalilin da ya sanya aka ki aminta da shi.
A wani labarin kuma an kubutar da wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su bayan wani artabu tsakanin mafarauta da masu garkuwa da mutane a dajin Chida da ke karamar hukumar Kuje a babban birnin tarayya, Abuja.
Shugaban mafarautan, Adamu Usman, ya bayyana haka a lokacin da yake mika wadanda aka ceto ga shugaban Kuje, Abdullahi Suleiman Sabo, a sakatariyar majalisar a ranar Talata.
Daya daga cikin wadanda aka ceto, Adamu Ibrahim Takwa, ya ce an yi garkuwa da shi ne a hanyar Takwa-Kwaku a lokacin da yake dawowa daga cin kasuwa ranar Lahadi.
Ya ce masu garkuwa da mutanen sun dauke shi da abokin aikinsa zuwa wasu tsaunuka da koramai inda suka isa maboyarsu a dajin Chida.
Shugaban Kuje, Sabo, ya ce za su ci gaba da yin iya kokarinsu wajen ganin an shawo kan matsalar garkuwa da mutane a yankin.
Yayin da ya yaba wa mafarauta bisa kokarin da suka yi na ceto wadanda abin ya shafa.
Sabo, wanda shi kuma ya mika wadanda abin ya shafa ga iyalansu, ya bukace su da su kula da harkokin tsaro, su tabbatar sun kai rahoton wasu abubuwa da faruwa cikin al’ummarsu ga jami’an tsaro.
Leadership Hausa tattaro cewa tun da farko masu garkuwa da mutane sun bukaci a biya su kudin fansa Naira miliyan 10..
Source LEADERSHIPHAUSA