Kamar yadda gidan jaridar vangurd suka rawaito a wani taron manema labarai da kungiyar mazauna babban birnin tarayyar abujan suka gabatar sun bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta bukatar da suka nema wacce suke ganin hakan ne kawai zai tabbatar da dorewar zaman lafiya ga mazauna babban birnin tarayyar dama wadanda suke bakuntar babban birnin domin uzurori mabambanta.
Tun da farko mazauna abujan sun bayyana jinjinar su babbar kotun tarayya dake kaduna dama bangaren shari’a na tarayyar najeriya bisa namijin kokarin da sukayi na tabbatar da gaskiya ta hanyar sakin sheikh ibrahim zakzaky da mai dakin sa malama zinatuddin.
Sai dai mazaunan na Abuja sun bukaci gwamnatin tarayya karkashin shugaba muhammadu buhari da ta gaggauta sakin fasfunan sheikh zakzaky da mai dakin sa domin su tafi neman magani.
Kungiyar ta mazauna Abuja ta tabbatar da cewa, ta samu masaniya cewa bayan sakin malam zakzaky sun dawo birnin na abuja shi da mai dakin sa da niyya barin kasar domin zuwa neman lafiya a kasar da ta dace sakamakon lalacewar asibitocin cikin gida da ake dasu amma sai dai tafiyar shehin malamin ta gamu da cikas sakamakon fasfo din sa dana mai dakin sa dake hannun hukumomin gwamnati wanda hakan ya hana su tafiya domin neman maganin a kasashen ketare.
”Abuja ta kasance muhalli mai tsari da kwanciyar hankali, amma bayan tsare malam zakzaky da kuma soma jerin gwanon lumana da mabiyan sa suka dingi yi garin abuja ya koma kamar wani filin yaki” Inji kungiyar ta mazaunan Abuja.
Sanarwar ta cigaba da cewa ba suna tuhumar almajiran malamin bisa fitowa jerin gwano domin aiwatar da damar da kundin tsarin mulki ya basu bane amma suna tsoron kada rashin sakin fasfunan malamin da mai dakin sa ya sanya almajiran nasa su dawo bisa kwalta wanda hakan babban ci baya ne duba da yadda daga sakin malamin zuwa yanzu abubuwa suka fara komawa dai dai a babban birnin tarayyar na Abuja wanda ya shaidi matsaloli kala kala wanda suka hada da rasa rayuka, durkushewar sana’o’i da sauran su duk sakamakon rike malamin da gwamnati tayi.
Sanarwar ta mazauna Abuja ta bukaci gwamnati ta gaggauta sakin fasfunan malamin da mai dakin sa domin samun zaman lafiya mai dorewa a babban birnin tarayyar na Abuja.