Matar tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ta roki gwamnatoci su taimakawa masu fama da cutar sukari.
Bola Obasanjo ta halarci wani taro da matasa suka shiryawa wadanda suke dauke da ciwon suga daga yankunan kasar nan.
Mai dakin ta Cif Olusegun Obasanjo tayi kira ga masu larura su rika kiyaye dokoki da kuma sharudan malaman asibiti.
Matar tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, Bola Obasanjo tayi kira ga gwamnatoci a kowane mataki su kula da masu ciwon sukari.
Punch ta rahoto Misis Bola Obasanjo tana cewa ya kamata gwamnatoci su rika daukar dawainiyar marasa hali da suke fama da ciwon sukari.
Matar tsohon shugaban tace kudin da ake kashewa wajen maganin ciwon sukari yana da matukar yawa, don haka marasa lafiya ke neman taimako.
Jaridar tace dattijuwar tayi wannan bayani ne a wajen wani taron kwana biyu da matasan jigar Ogun suka shirya a cibiyar Talabi Diabetes Centre.
Kamar yadda muka samu labari, taron ya samu halarcin mutane 29 daga kowane yanki na kasar nan.
Kira ga mutanen jihar Jigawa Mai dakin Obasanjo ta fadawa masu fama da ciwon da suka zo daga jihar Jigawa ya kamata kwamishinoni da gwamnati ta taimaka masu da magani.
Bola Obasanjo take cewa cutar sukari na da tsadar kula, kuma za a iya cewa bai da tsada sosai.
Abin da kawai za a iya shi ne a nemi taimakon hukuma. “Idan ba ku fada masa ba, su (gwamnatoci) ba za su sani ba.
Akwai abubuwa da yawa a gabansu. Sai kun sanar da su tukuna, sai su taimaka maku.”
Bola Obasanjo Baya ga neman taimako, Bola Obasanjo ta bada shawara ga mahalarta taron da suyi amfani da shawarwarin da masu rayuwa lafiya kalau da cutar suke ba su.
Mai gidanta Obasanjo yana cikin wadanda sun dade su na fama da ciwon sukari, amma har yau yana rayuwarsa saboda ya kiyaye abin da Likitoci suke fada.
Gwamna zai koma mawaki A baya kun ji labari Gwamna Oluwarotimi Akeredolu yace abin da yake hari da zarar ya bar kan kujerar Gwamnan Ondo shi ne ya zama fitaccen mawakin coci.
Oluwarotimi Akeredolu wanda kwararren Lauya ne yake cewa zai koyi amfani da fiyano domin ya rika rera wakokin bege a matsayinsa na mai kunar Yesu.
Source: LEGITHAUSA