Da zarar mace ta samu juna biyu, akwai matakan da suka dace a dauka domin tarairayar wannan ciki, don gudun ka da ta afka hatsarin gamuwa da barewar juna biyun ko kamuwa da wasu cututtuka wadanda za su iya shafar uwar ko abin da take dauke da shi.
A bangaren abinci, akwai tsarin yanayin abinci ko cima wadanda suka dace mai ciki ta riga ci ko yin amfani da su, domin samun nagartatacciyar lafiya, rashin cin ire-iren nau’o’ikan wannan abinci, na iya haifar da rasa wasu sinadaran jiki ko kuma yawaitar su; daga karshe kuma su haifar da matsaloli iri daban-daban.
Rukunin ire-iren abincin da muke amfani da su; kowanne na da irin aiki ko amfanin da yake da shi a jikin Dan Adam, don haka ba za ka yi amfani da dangin abinci guda daya ba; sannan ka yi tsammanin cewa za ka samu aikin sauran dangogin abinci baki-daya ba.
Har ila yau, mata masu ciki na bukatar zuwa Awo domin a tabbatar da cewa ba su da wata matsala, sanadiyar daukan wannan ciki. Sannan a yi kokarin fahimtar da su wajen bin tsarin amfani da abinci a kimiyance.
Abinci mai dauke da sinadarin ‘Carbohydrate’, daya daga cikin babban aikinsa shi ne, samar da kuzari, karfi da kuma garman jiki. Saboda haka, ana bukatar mata masu ciki su rika amfani da dangogin ire-iren nau’o’in abinci masu dauke da ‘Carbohydrate’.
Haka zalika, ya kyautu mata masu dauke da juna biyu su rika amfani da ‘Bitamins’, ma’ana wajibi ne masu ciki su rika amfani da duk wani nau’in kayan abinci, wadanda suka kunshi ko suke tattare da sinadarin ‘Bitamins’.
Dalili kuwa, wannan ‘Bitamins’ na kara kuzari da samar da wadataccen jini tare kuma da kare jiki daga fada wa karancin ko rashin jini, sannan yana kara kyan fata da jiki da kuma sa cin abinci da sauran makamantansu.
Sai kuma sinadarin ‘Protein’, idan aka yi dace mace mai juna biyu ba ta da wata matsala, ana bukatar ta rika yin amfani da kayan abinci, wadanda ke dauke da rukunin sindarin ‘Protein’; domin assasa samun garkuwar jiki.
Kazalika, ana so mace mai ciki ta kiyaye wannan tsari; ba kasafai ake so ta yawaita amfani da kitse ko dangoginsa ba, sai dai idan bukatar hakan ne ya taso.
Har ila yau, ana so mai dauke da juna biyu ta rika yin ta’ammali da abinci mai tsafta, sannan a koda-yaushe su rika zama cikin tsafta tare da tsaftace muhallin da suke zaune. Domin kuwa, shi ne zai taimaka mata ta haifi lafiyayyen jariri, mai dauke da koshin lafiya.
Sannan kowane irin nau’in abinci; indai har babu cikakkiyar tsafta a tare da shi, ba a bukatar sa ga mata masu ciki.
Source LEADERSHIPHAUSA