Kwalara ta kashe mutane 620 a Malawi tun bayan bullar cutar a farkon shekarar da ta gabata, in ji ministan lafiya Khumbize Chiponda.
A ranar Litinin, an tabbatar da adadin mutane 18,222 da suka kamu da cutar kwalara, yayin da kasar ta samu rahoton mutane 16,780 da suka warke, yayin da 822 ke ci gaba da zaman jinya a cibiyoyin da aka ware musu.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Chiponda ta kara da cewa a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, kasar ta samu rahoton mutane 409 da suka kamu da cutar, da karin mutane 25 da suka mutu, sai kuma wasu karin mutane 10 da ake zargin sun kamu da cutar.
“Dukkanin cibiyoyin lafiya 29 sun tabbatar da bullar cutar amai da gudawa, tun daga lokacin da ta barke a watan Maris a lardin Machinga,” in ji Chiponda.
A ranar Litinin ne gwamnatin kasar ta fitar da sanarwar cewa an rufe makarantu a fadin kasar, har sai lokacin da hali ya yi, sai dai za a iya budewa nan da makonni biyu a biranen Blantyre da Lilongwe.
Tun farko dai an shirya bude makarantu a ranar 3 ga watan Janairun 2023, amma kamarin cutarta kwalara ya tilastawa gwamnati daukar matakin, yayin da ake samun karuwar wadanda cutar ke kashewa.