Kwalara ta hallaka mutum 50 a Afirka ta Kudu
Hukumomin lafiya a Afirka ta Kudu sun gargaɗi mazauna lardin Gauteng da ke ƙasar da su yi taka tsantsan game da amfani da ruwan da suke sha a daidai lokacin da ɓarkewar cutar kwalara ya hallaka kusan mutum 50.
Ƙungiyoyi al’umma sun bukaci gwamnati da tashi tsaye don inganta da kuma samar da tsaftataccen ruwan sha.
Galibin mace-macen da aka samu a cikin makonni shida da suka gabata, sun faru ne a yankin Hammanskraal, inda mazauna yankin suka ce sun shafe makonni suna cikin wahala wajen ganin sun samu ruwa mai tsafta.
Sai dai suna cikin hana kwatsam aka samu bullar cutar a faɗin ƙasar.
Ruwan famfo da ake samu ya kasance ba shi da tsafta a yankuna da dama, inda ya zama tilas mutane suka koma dogaro da motocin dakon ruwa da gwamnati ke samar wa.
Cutar kwalara, wadda gurɓatacciyar abinci da ruwa ke haddasa yaɗuwarsa, na haifar da gudawa da amai kuma mutum na iya mutuwa cikin sa’o’i idan bai samu agajin gaggawa ba.
Read more :
Abin da ya sa ake tuhumar gwamnatocin baya kan ‘kuɗin Abacha’.
Shahadar wani Bafalasdine da sojojin yahudawan sahyoniya suka harbe.
Moscow: Amurka ta amince da aikata laifukan yaki.